1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu wata alaka tsakanin Saddam Hussein da kungiyar Al-Qaida

September 9, 2006
https://p.dw.com/p/Buk4
Wani bincike da majalisar dattijan Amirka ta yi ta gano cewa ba bu wata alaka tsakanin Iraqi karkashin Saddam Hussein da kungiyar ´yan takife ta al-Qaida. Rahoton da majalisar dattijan ta bayar ya ce daidai da rana daya Saddam bai taba taimakawa Al-Qaida da kudi ko kayan aiki ba hakazalika ba ta ba yin wata hulda da tsohon shugaban Al-Qaida a Iraqi ba wato Abu Mussab al-Zarqawi ba. Daga cikin hujjojin da ya bayar gabanin ya kaddamar da yaki kan Iraqi a shekara ta 2003, shugaba Bush ya ce da akwai dangantaka tsakanin tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein da kungiyar al-Qaida. Wakilan jam´iyar Democrat sun ce rahoton ya nunar a fili cewa shugaba Bush bai da wata hujjar yin wannan yaki.