1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu wani ci-gaba da aka samu a kokarin rage talauci a Afirka

June 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuJd

Duk da kwarkwayan ci-gaban da ake samu MDD ta ce har yanzu ana tafiyar hawainiya a kokarin rage talauci a kasashen Afirka kudu da Sahara. A ckin wani rahoto na wucin gadi da ta bayar MDD ta ce ba za´a cimma buri ko da guda daya ba na shirin tallafawa kasashe masu tasowa wato Millenium Development Goals kafin shekara ta 2015. A cikin shekara ta 2000 aka amince da shirin mai rukunai guda 8 da nufin auna duk wani ci-gaba da ake samu wajen rage radadin talauci. Rahoton ya ce sama da kashi 41 cikin 100 na mazauna kasashen Afirka kudu da Sahara na rayuwa akan kudi da a kasa dala daya a rana. Bugu da kari yawan mutane dake mutuwa sakamakon cutar AIDS ko Sida na ci-gaba da karuwa tun bayan amnice da shirin. An fid da wani sashe na rahoton ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen kungiyar G8 ke taron kolin su a nan Jamus. MDD ta ce ya zama wajibi kasashe masu bai da taimakon raya kasa dauki matakan gaggawa idan suna son su ika alkawarin da suka a shekara ta 2005 na ninka yawan taimako ga nahiyar Afirka kafin shekara ta 2010.