Babu tabbas game da rasuwar Izzat Ibrahim al-Douri | Labarai | DW | 13.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu tabbas game da rasuwar Izzat Ibrahim al-Douri

A wata ziyara ta ba zata da ya kaiwa Iraqi babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi kira ga al´umomin kasar da ke rikici da juna da su nemo hanyar yin sulhu. Annan ya ce yin haka ya na da muhimmanci ga makomar kasar. Annan ya sanar da cewa a cikin watan janeru za´a gudanar da taron wanzar da zaman lafiya a Iraqi kamar yadda kungiyar kasashen Larabawa ta nema. Wannan ziyarar dai ita ce ta farko da babban sakataren ya kai Iraqi tun bayan kifar da gwamnatin Saddam Husein shekaru biyu da rabi da suka wuce. A wani labarin kuma magoya bayan jam´iyar Baath a Iraqi sun buga rahotanni masu sabawa juna a shafin su na intanat game da rasuwar mukaddashin Saddam Hussein wato Izzat Ibrahim al-Douri. Bayan tabbatar da rasuwarsa a wani sakon intanat, wani sakon na dabam da ya nemi gafara a kann wannan kuskure inda ya ce malam al-Douri na nan da ransa. Shi dai na hannun daman Saddam din shi ne babban jami´in tsohuwar gwamnatin Iraqi da har yanzu bai shiga hannu ba. Ana yi masa kallon babban mai taimakawa masu ta da kayar baya Iraqi kuma shi ne na 6 a jerin mutanen da Amirka ke nema ruwa a jallo.