1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu tabbacin ranar komawar Buhari gida

Yusuf Bala Nayaya
February 21, 2017

Har kawo yanzu an kasa sanin hakikanin cutar da ke damun Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya daga jami'an gwamnati, abin da ke haifar da mabanbantan tambayoyi kan hakikanin halin da yake ciki.

https://p.dw.com/p/2XyXY
Paris Medef Zentrale Buhari Gattaz
Hoto: Getty Images/AFP/E. Piermont

Mahukunta a Najeriya sun bayyana cewa babu abin tashin hankali a dangane da batun rashin lafiyar shugaba Muhammadu Buhari sai dai ta ce shugaban zai tsawaita lokacin dawowarsa gida, bayan da ya je asibiti a Birtaniya domin a duba lafiyarsa. 

A cewar fadar gwamnatin Najeriyar Shugaba Buhari ya je ne domin a duba lafiyarsa da aka saba yi duk shekara, kuma sakamakon gwajin ya nunar da cewa shugaban na bukatar hutu. Fadar dai ba ta yi karin haske kan ko yau she ne shugaban zai koma gida Najeriya ba. Da fari dai fdar gwamnatin ta sanar da cewa Shugaba Buharin mai shekaru 74 a duniya zai kwashe kwanaki 10 ne kacal a Birtaniyan domin a duba lafiyarsa, yayin da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da ke da shekaru 59 a duniya zai ci gaba da jan ragamar mulkin kasar. Har kawo yanzu dai, babu wani cikakken bayani kan irin cutar da ke damun shugaban kasar ta Najeriya daga jami'an gwamnati, abin da ke haifar da mabanbantan tambayoyi kan hakikanin halin da yake ciki.