1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu ramuwar gayya a cewar Israela

April 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1Y

Rahotanni daga Israela na nuni da cewa mahukuntan kasar ba zasu dauki matakin soji na ramuwar gayya ba akan hukumar Palasdinawa, a game da harin kunar bakin waken nan da aka kai birnin Tel Aviv.

Harin kunar bakin waken daya haifar da rasuwar bani yahudu tara da kuma jikkata wasu 50, a yanzu haka na ci gaba da fuskantar Allah wadai daga kasashe daban daban na duniya.

Ya zuwa yanzu dai tuni, mahukuntan na Israela suka zargi hukumar Palasdinawa karkashin Jagorancin kungiyyar Hamas da hannu a cikin kai wannan hari.

Ya zuwa yanzu dai kasar Japan ta shiga sahun kasashe dake kokarin dakatar da irin tallafi na raya kasa da suke bawa yankin na Palasdinawa, har zuwa lokacin da zasu rungumi tafarki na zaman lafiya.