1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu gudu babu jada baya.. inji ma´aikata a Zimbabwe

September 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bujc

Jami´an yan sanda a Zimbabwe , sun hana kungiyyar kwadagon kasar gudanar da wata zanga zanga, data shirya yi a yau din nan.

Jami´an yan sandan , sun baza jami´an nasu ne a manya manyan titunan birnin Harare da kuma sauran manyan titunan kasar, don tabbatar da cewa, zanga zangar bata gudana ba kamar yadda aka tsara.

A dai lokacin wannan sintiri , rahotanni sun shaidar da cewa yan sandan sun cafke masu kokarin aiwatar da zanga zangar a kalla 135, a gurare daban daban na kasar.

Kafin dai daukar matakin hana gudanar da zanga zangar ta yau, a can baya jami´an tsaron kasar sun haramtata da cewa ta take dokokin kasar da suka shafi harkokin tsaro

Rahotanni dai sun rawaito shugaban kungiyyar kwadagon kasar, wato Mr Thabita Khumalo na fadin cewa matakin da yan sandan suka dauka ba zai tsorata su ba.

Kungiyyar kwadagon dai ta shirya gudanar da wannan zanga zangar ne, don neman karin albashi ga ma´aikatan kasar, don samun sukunin daidaita sahu da tsadar rayuwa dake addabar su.

.