Babu canji akan halin rashin lafiyar da Mista Sharon ke ciki | Labarai | DW | 06.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu canji akan halin rashin lafiyar da Mista Sharon ke ciki

Likitoci da ke yiwa FM Isra´ila Ariel Sharon mai fama da mummunan rashin lafiya jiyya a asibitin Hadassah dake Birnin Kudus sun ce har yanzu ba wani canji a halin da FM na Isra´ila ke ciki. Likitocin sun ce har yanzu FM na cikin wani hali na rai hannun Allah kuma za´a ci-gaba da sanya masa nau´rar tallafawa numfashi har nan da sa´o´i 24 masu zuwa. FM dai na cikin wannan hali ne kwana daya baan da likitoci suka yi masa tiyata don tsayar da jinin dake zuba a cikin kwakwalwarsa sakamakon mummunar mutuwar jiki da ya fuskanta da kuma zubar jini a cikin kwakwalwa. Rahotannin dai sun nunar da cewa FM na Isra´ila ba zai iya sake komawa bakin aikin sa ba ko da ya farfado daga wannan rashin lafiya na mutuwar jiki.