Babu alamun sakin tsohon shugaba Tanja | Siyasa | DW | 26.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Babu alamun sakin tsohon shugaba Tanja

Al'ummomin Niger na ci gaba da martani dangane da jawabin shugaban majalisar tuntuɓar juna

default

A Jamhuriyar Nijar ana ci gaba da mayar da martani game da jawaban da shugaban majalisar tuntuɓar juna yayi wa kafofin yaɗa labarai na ketare, inda ya gargaɗi magoya bayan tsohon shugaban kasa Tanja Mohammadou. Lokacin jawabin na shi jami´in ya ce idan har magoya bayan tsohon shugaban suka ci gaba da neman a sake shi, hakan yana iya sanya tilas a ɗauke shi daga inda yake yanzu zuwa wani gidan kurkuku mai tsanani a ƙasar.

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa

Sauti da bidiyo akan labarin