1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu alamar cimma tudun dafawa a taron kare muhalli a birnin Bali

December 13, 2007
https://p.dw.com/p/Cb1m
Babu alamar cimma wata madafa kwana guda gabanin a kammala babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya akan muhalli a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia. Shugaban hukumar kula da sauyin yanayi na MƊD Yvo de Boer ya ce ya damu ƙwarai da gaske a dangane da tattaunawar a Bali cewa ba za a cimma wata yarjejeniyar yaƙi da ɗumamar yanayi. Batun da har yanzu ake taƙaddama a kai shi ne ko ya kamata a shimfiɗa kwararan ka´idoji a cikin sabon daftarin yarjejeniyar kare muhalli ta duniya a game da rage fid da gurbataccen hayaƙi. Kasar Amirka dai ke kan gaba wajen nuna adawa da wannan shiri. Ita kuwa Jamus da sauran ƙawayenta na ƙungiyar tarayyar Turai na goyon bayan sanya ƙwaƙƙwaran burin rage fid da hayaƙin dake ɗumama doron ƙasa.