Babu alamar cimma daidaito a taron kungiyar WTO a Hongkong | Labarai | DW | 17.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu alamar cimma daidaito a taron kungiyar WTO a Hongkong

An shiga tattaunawa ta karshe a babban taron kungiyar cinikaiya ta duniya WTO a Hongkong, inda ake ci-gaba da cece-kuce tsakanin kasashe matalauta da masu arziki. A yau asaba rana ta biyar a wannan taro ba´a ga wata alamar cimma wani tudun dafawa a takaddamar da ake a fannin aikin noma musamman game da tallafi da kuma kara bawa kasashe masu tasowa damar shigar da kayakin su a kasuwannin kasashe masu ci-gaban masana´antu ba. A jiya juma´a an yi kusan tashi baram baram a taron, inda mahalarta taron suka bayyana da cewa mummunan matsala. KTT na sha suka game da kin da ta yi na sanya lokacin da zata rage yawan tallafin da take ba manomanta.