Babbar wakiliyar Amirka ta tattauna da hukumomin Kenya | Labarai | DW | 05.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babbar wakiliyar Amirka ta tattauna da hukumomin Kenya

Ministar Raya ƙasa ta Jamus, Heide-Marie Wieczorek-Zeul ta yi kira ga gwamnatin Kenya da shugabannin adawa da su sasanta rikicinsu ta hanyar tattaunawa. Wiezerok-Zeul ta ce ta goyi bayan shawarar Prain-Minitan Britaniya Gordon Brown na kafa gwamnatin hadin-gwiwa tsakanninsu. A halin yanzu dai, fadar gwamanti dake Berlin ta sanar cewar zata aikawa ƙungiyar taimako ta Red Cross ta Kenya taimako na Euro dubu dari uku don tallafawa al’uman Kenya wadanda rikicin ya rutsa da su. A halin yanzu kuma, Sakatare Janar na MDD Mr. Ban Ki-Moon ya yi magana da shugaba Mwai Kibaki tare da abokin adawarsa, Raila Odinga, ta wayar talho, inda ya bukacesu da su tattauna da juna don cimma sulhu. Rikicin da ya tashi jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben, ya yi sanadiyar mutuwan mutane da dama, kana ya sa wasu dubu dari biyu suka rasa gidajensu. Bugu da kari, a kokarin da kasashen duniya ke ci gaba da yi na neman bakin zaren war-ware rikicin na Kenya, wakiliyar Amirka a harkokin Afirka Jandaye Frasser yanzu hak ata sadu da shugabar adawa Raila Odinga a birnin Nairobi kuma ta nemi ganawa da shugaba Kibaki kann batun daidaita sabanninsu.