1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babbar mota ta halaka mutane 12 a kasuwar Kirsimeti a Berlin

Yusuf Bala Nayaya
December 20, 2016

Mutumin da ya tuka motar ana zargin ya shigo kasar ne cikin 'yan gudun hijira daga kasar Pakistan ko Afghanistan kamar yadda jami'an tsaro suka fada wa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA.

https://p.dw.com/p/2UZk3
Deutschland Polizei geht von Anschlag auf Berliner Weihnachtsmarkt aus
Hoto: Reuters/F. Bensch

Mutane 12 ne suka rasu yayin 48 suka samu raunika bayan da wata babbar mota ta kutsa kai cikin dandazon jama'a a wata kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus, abin da ake zargin akwai alamu na cewa hari ne na ta'addanci.

Shi dai direban wanda da farko ya tsere amma daga bisani aka cafke shi a wani wuri mai tazarar kilomita kalilan daga kasuwar Kirsimetin da ke a gaban cocin nan mai dadadden tarihi na tunawa da Kaiser-Wilhelm da kuma ke dab da titin Kurfürstendamm daya daga cikin manyan wuraren hada-hadar masu saye sayarwa a birnin na Berlin, ana kyautata cewa ya shigo Jamus ne cikin watan Fabrairu a matsayi dan gudun hijira ko dai daga Afghanistan ko kuma Pakistan.


Ko da yake ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere bai fito karara ya bayyana harin da cewa na ta'addanci ba ne, amma ya ce ai dama biri ya yi kama da mutum.

Deutschland Anschlag mit LKW auf Weihnachtsmarkt in Berlin
Hoto: Reuters/F. Bensch


Ya ce: "A bangaren gwamnatin Jamus mun kadu da wannan labari. Muna mika ta'aziyarmu ga 'yan uwa da iyalan wadanda suka rasu, muna fata wadanda suka samu raunika za su samu sauki. Yanzu haka an baza 'yan sanda a wurin, muna kuma gudanar da bincike kan wanda ake zargin. Ba mu da masaniya ta karshe yanzu kan dalilan aukuwar wannan lamarin amma ba za mu nuna gajiyawa ba har sai mun tantance gaba daya. Saboda haka ba zan iya cewa hari ne na ta'addanci ba ko da yake alamu na nuna haka."

Shi ma kakakin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wato Steffen Siebert ya wallafa a shafin Twitter cewa suna juyayin wadanda suka rasu kana suna fata wadanda suka samu raunika za su samu taimakon da suke bukata cikin gaggawa.

Wani mutum da aka gano mace a kujerar gaban babbar motar mallakin wani kamfanin kasar Poland, daga baya an tabbatar cewa dan kasar ta Poland ne. Sai dai ba a san abin da ya yi ajalinsa ba. An dai jiyo mai kamfanin Ariel Zurwaski na fada wa tashar telebijin ta Poland cewa motar na hannun wani dan uwansa ne tun ranar Litinin da rana, zai kai karafa birnin Berlin, amma ba su ji duriyarsa ba tun da la'asar. Motar kuwa ta kutsa cikin dandazon mahalarta kasuwar ta Kirsimeti ne wajejen karfe takwas na yamma.

Deutschland Anschlag mit LKW auf Weihnachtsmarkt in Berlin
Furanni da kyandura don juyayin wadanda suka rasu a kasuwar ta KirsimetiHoto: Reuters/F. Bensch

Michael Müller shi ne magajin garin birnin Berlin da ya nuna kaduwarsa dangane da abin.

Ya ce: "Wannan lamari ne mai sarkakiya. Abin takaici ne irin wannan abu ya faru a wannan lokacin na hada-hadar bikin Kirsimeti. Yanzu muna shaida iri munanan abubuwan da abokanmu suka shaidar a wasu kasashen."

Wasu faifayen bidiyo da aka dauka jim kadan bayan harin kuma aka watsa ta gidaje telebijin din Jamus da dama sun nuna yadda mutane da suka jimu kwance a kasa yayin da ake yi ta jin karar jiniyar motocin 'yan sanda.

Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a fadin babban birnin na Jamus wato Berlin yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike. Matukar aka tabbatar hari ne na ta'addanci to ke nan lamarin ya zo ne kasa da da watanni shida bayan wasu tagwayen hare-hare a Jamus da ke da asali daga masu koyi da manufofin kungiyar IS.

Kasashe da dama ciki har da Amirka da Faransa sun yi Allawadai da lamarin, ita ma kungiyar EU ta yi tir da harin.