1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babbar gwamnatin hadin guiwa

October 14, 2005

A shekarar 1966 aka kafa babbar gwamnatin hadin guiwa karo na farko a Jamus

https://p.dw.com/p/BvYk

A ranar daya ga watan desamban shekarar 1966 aka yi wa Kurt Georg Kiesinger mubaya’a a matsayin shugaban wata gwamnatin hadin guiwa ta farko da aka kafa tsakanin ‚yan Christian Union da ‚yan Social Democrats. Makonni kalilan kafin haka mulkin hadin guiwa tsakanin ‚yan Christian Union din da Free Democrats a karkashin Ludwig Erhard ya wargaje sakamakon mummunan sabanin da aka fuskanta tsakanin sassan biyu akan maganar haraji. ‚Yan Free Democrats sun kakkabe hannunsu daga gwamnatin ne saboda ‚yan Christian Union na da ra’ayin tsawwala haraji. Bayan rushewar gwamnatin sai aka samu kusantar juna tsakanin Christian Union da Social Democrats, wadanda gaba daya suke da wakilai kusan 450 a majalisar dokoki, a yayinda ita jam’iyyar adawa daya kwal ta Free Democrats ke da wakilai 49 kacal a majalisar. A wancan lokaci kuwa mutane sun shiga tababa a game da irin rawar da wannan ‚yar karamar jam’iyya zata taka a matsayinta na ‚yar hamayya a majalisar dokokin ta Bundestag ta la’akari da cewar yawan wakilan nata bai taka kara ya karya ba. Shi kansa shugaban gwamnatin da aka nada Kurt Georg Kiesinger sai da ya lura da wannan sabuwar kalubala da siyasar Jamus ta samu kanta a ciki, inda jam’iyyar adawa ba ta da wani tasiri na a zo a gani, a sakamakon haka a lokacin da ake masa mubaya’a yake cewar:

Muhimmin abin da ake bukata a irin wannan hali na babbar gwamnatin hadin guiwa shi ne sanin ya kamata wajen tafiyar da mulki, ka da a nemi yin amfani da madafun iko ta hanyoyin da ba su dace ba.

A daidai wannan lokacin ne kuwa aka samu wani sabon ci gaba a cikin tarihin siyasar Jamus, inda aka samu hadin kakkarfan hadin kai tsakanin dalibai da manyan masana da mawallafa domin adawa da duk wani mataki na gwamnati da zai kai ga kawo canji ga daftarin tsarin mulkin kasar. An fuskanci zanga-zanga mai tsananin gaske, wacce ta zama ruwan dare a duk fadin Jamus domin adawa da yakin Vietnam da ita kanta gwamnati. Wani da ake kira Rudi Dutschke ya kasance daya daga cikin shahararrun shuagabannin daliban a wancan lokaci ya kuma yi bayani yana mai cewar:

Tilas ne mu fito mu bayyana adawa ga wata majalisa wadda ba ta magana da yawunmu saboda ba mu da wakilci a cikinta. Wajibi ne mu kalubalanci wannan babbar gwamnati ta hadin guiwa wadda ta kunshi gaggan jam’iyyun siyasa guda biyu mai fafutukar tabbatar da angizonta, yadda ta dama haka za a sha in da zaki ko da tsami.

A hakika kuwa gwamnatin ta samu kyakkyawar nasara wajen farfado da tattalin arzikin kasa sakamakon kakkarfan hadin kai da aka samu tsakanin ministan kudi na Christian Union da ministan tattalin arziki dan Social Democrats.