Babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince da kudirin hana yaduwar kananan makamai | Labarai | DW | 07.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban zauren majalisar dinkin duniya ya amince da kudirin hana yaduwar kananan makamai

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ba tare da son ran Amurka ba, ya amince da wani kuduri da zai kai ga samarda yarjejeniyar farko ta kare yaduwar cinikin kananan makamai ta kasa da kasa.

Kudirin ya bukaci sakatare janar na majalisar dinkin duniya daya nemi shawarar kasashe 192 membobi game da yiwuwar samarda yarjejeniya game da shige da fice na kananan makamai.

Ya kuma bukaci sakatare janar din daya mika rahotonsa a babban taro na zauren nan gana a shekara mai zuwa.

Kasashe 153 suka amince da wanan kuduri kasashe 24 suka janye yayinda kasar Amurka ita kadai ta jefa kuriar kin amincewa.