Babban taron tattalin arziki na duniya | Siyasa | DW | 25.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Babban taron tattalin arziki na duniya

Manyan shugabanin kasashen duniya,yan kasuwa da manyan yan siyasa ne suka taru a garin Davos na kasar switzerland,domin tattauna hanyyoyin karfafa tattalin arziki a duniya.

default

wajen wani taron manema labarai kafin bude taron a yau,babban jamii kuma wanda ya kafa wannan zaure,Klaus Schwab,ya sanar da cewa,daya daga cikin muhimman batutuwa da taron zai maida hankali a kansa shine,mayarda huldar kasuwancin daga yammacin duniya zuwa kasashen gabashin duniya,inda yace zaa duba kasashen Sin da India a matsayin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki.

Tun lokacinda aka kirkiro da wannan zaure a 1971,abinda yake yi shine hada manyan yan kasuwa na kasa da kasa da manyan yan siyasa da kwarraru a fannin tattalin arziki,domin su tattauna hanyoyin karfafa tattalin arzikin kasashen duniya.

Schwab yace,zauren,yana taka rawar gani,saboda gwamnatoci,yan kasuwa da manyan yan siyasa suna zama tare domin magance batutuwa da suka shafi tattlin arzikin kasashen duniya.

Sai dai Andreas Missbach na wata kungiyar kare hakkin bil adama,yace wannan haramtaccen taro ne,saboda a cewarsa,ya kunshi manyan yan siyasa da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa,inda yace manyan kanfanoni ne da sauran yan kasuwa suke cin moriyar taro irin wannan.

Taron haka zalika zai tattauna batutuwan siyasa,yankin gabas ta tsakiya,batun Iran da yankin gabas ta tsakiya,addinin musulunci da wasanni.

Taron na yau zai kuma mayarda hankali akan ci gaban kimiya da yadda ta shafi kasuwanci a duniya.

Kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Switzerland sun zargi gwamnatin kasar da kasha makudan kudade a fannin tsaro,wajen wannan taro,daya hada da manyan shugabanin kasashen duniya.

Andre Shneider,daya daga cikin darektocin taron ya tabbatar da cewa,ta kebe dala miliyan 6 da dubu dari da hamsin wajen tsaro,yayinda kuma ta girke sojoji 5,000 da zasu tabbatar da tsaro wajen wannan taro,wanda yake samun suka da zanga zanga a kowace shekara.

Kodayake a wannan karo kungiyoyi masu zaman kansu na kasar sunce ba zasu yi zanga zangar a cikin garin Davos din ba,amma zasuyi a wasu wurare dabam na cikin kasar.