1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron tashar DW na 2016 ya kawo karshe

Lateefa Mustapha Jaafar/ SBJune 15, 2016

A yayin taron na "Global Media Forum", masana a fannoni daban-daban sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi kare hakkin dan Adam musamman 'yan jarida da ma ci gaban al'umma.

https://p.dw.com/p/1J7DP
GMF Panel 50 How art and culture can foster...
Babbann zauren da ake tattauna batutuwa a taron DWHoto: DW/K. Danetzki

Masu fashin baki da masu fafutuka da suka halarci zauren tattaunawa kan rawar da kafafen yada labarai ka iya takawa wajen yaki da cin zarafin mata sun tabo batutuwa da dama da suka danganci wannan matsala musamman a kasashe masu tasowa da ma wadanda suka ci gaba. Mahalarta da ma manazartan da suka halarci wannan zaure, sun fito ne daga kasashe akalla 100 na duniya.

Rasha El-Ibiary malama a fannin siyasa da sadarwa da kuma jinsi a jami'ar Future da ke Masar. ta ce ya zamo wajibi kafafen yada labarai su fitar da wani tsari na kyautata wa mata musamman wadanda aka ci zarafinsu yayin bayar da rahotanninsu:

Global Media Forum 2016 in Bonn - gemischte Teilnehmer
Daya daga cikin mahalarta taron daga kasashen LarabawaHoto: DW/N. Martin

"Ya kamata a samu wakilci mai ma'ana a kafafen yada labarai ta fuskar cin zarafi. Kamata ya yi a rinka nuna matan da aka ci zarafinsu a matsayin wasu wadanda suka tsira kuma gwarzayen al'umma maimakon a rinka nuna su a matsayin kaskantattu wandan suka fuskanci duka ko kuma fyade. A kafafen yada labarai an fi mayar da hankali kan matsalar da matan suka samu mai makon nuna irin yadda za a yaki wannan dabi'o'i, hakan na kara ta'azzara al'amuran ne kawai maimakon rage su."

To sai dai a cewar Kristina Lunz, ta jami'ar Oxford da ke Jamus kana mai gangamin yaki da cin zarafin mata kuma wadda ta samar da kungiyar gangamin 'StopBildSexism', da ke nuna kyama ga yadda ake buga hotunan tsiraici na mata, ba wai duka da fyade ne kawai cin zarafi ba, kuma ma kafafen yada labaran ba su ma fara yakar cin zarafin matan ba kasancewar su da kansu na buga hotunan mata kusan tsirara a jaridu da mujallu, wanda a ganinta shi ma cin zarafin mata ne.

Ita ma Christine Brendel manajar shirin kawo karshen cin zarafin mata ta yankin Latin Amirka a Hukumar Raya Kasashe ta Jamus GIZ ta bayyanar da cewa cin zarafin mata ya kasu kashi-kashi, kana ba wai matsala ce kawai ta kasashe ko bangare daban ba, kuma ya zama dole a kawo karshe:

"Cin zarafin mata matsala ce ta duniya baki daya ba wai matsala ta kasashe masu tasowa kawai ba, matsala ce ta kasashen da suka ci gaba, kana matsala ce ta kowanne yare ko kabila ko addini. Ta riga ta zama ruwan dare gama duniya, wannan abu ne mai muhimmanci da ya kamata a sani."

Panel Afrika GMF Judith Owigar
Judith Owigar daga kasar KenyaHoto: DW/K. Danetzki

Ko da yake a iya cewa a wannan zaure an tattauna matsala da ta shafi mata, sai dai maza ma sun samu halarta. Vincent-Immanuel Herr, marubuci ne kuma mai fafutuka na kungiyar HerrundSpeer, da ke birnin Berlin na Jamus, ya ce idan da so samu ne zai yi fatan a kawo karshen wannan matsalar nan ba da jimawa ba, sai dai ba abu ne da ya fara yau ba, don haka tilas a dauki lokaci kafin a kawo karshensa, kuma a ganinsa, maza ne ke da rawar takawa awajen kawo karshen wannan matsalar.