1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron MDD karo na 72

Ahmed Salisu
September 21, 2017

Babban taron Majalisar Dinkin Duniya na wannan shekarar ya fi maida hankalinsa ne kan kalubalen da 'yan Rohingya ke fuskanta da batun makaman kare dangi na Koriya ta Arewa.

https://p.dw.com/p/2kTNb
USA UN Sicherheitsrat
Hoto: picture alliance/dpa/L. R. Lima

Jawaban da shugabannin kasashen duniya suka gabatar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya tabo takaddamar da ake cigaba da yi kan makaman kare dangi da Koriya ta Arewa ke cigaba da yin gwajinsu da kuma matsalar da Musulmi 'yan kabilar Rohingya na kasar Myanmar ke fuskanta inda kasashen duniya da ma Majaliasar Dinkin Duniya ke cewar kisan da ake yi musu daidai ya ke da yunkuri na sharesu daga doron kasa.