1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan na jawabi akan daftarin sauye sauye da jakadu suka amince da shi.

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan

Shugabannin kasashen na duniya dake halartar babban taron majalisar dinkin duniya na da babban nauyi na yin cikakken nazari da kuma amincewa da daftarin sauye sauyen mai shafi 35 wanda jakadu a mashawartar majalisar suka zartar bayan tsawon watanni suna tafka muhawara a kan sa. Daftarin ya nemi samar da daidaito a tsakanin yaki da talauci a duniya da kuma kawar da ayyukan taádda, yayin da a daya hannun ya yi kokarin daukaka kare hakkin dan Adam da hana kisan kare dangi da aiwatar da gyaran fuska ga shaánin gudanarwar majalisar. Daftarin da jakadun suka amince da shi har ila yau, ya nuna a zahiri irin sabanin dake akwai tsakanin kasashe masu arziki da kuma kasashe matalauta akan batutuwa da dama da suka hada da batun kare hakkin bil Adama.

A waje guda dai manazarta na ganin cewa ba zaá ce an cimma nasara dari bisa dari ba, sai dai ace an sanya kyakyawar damba da zai wanzar da alhairi a nan gaba. A cewar jakadan Britaniya Emyr Jones a madadin kungiyar tarayyar turai daftarin ya yi nasara, kuma zai kasance kyakyawar shimfida ga taron shugabannin kasashen ta yadda zaá cimma bukatar da aka sanya a gaba. Shi kuwa jakadan Amurka a majalisar John Bolton yace a zahirin gaskiya basu sami yadda suke bukata ba daga wakilai 191 na majalisar, yana mai cewa ba abu ne mai sauki ba amma zasu yi aiki da abin da suka samu, yana mai cewa wannan ma mataki ne na cigaba.

Su kuwa kungiyoyin sa kai masu zaman kann su wadanda suma suka yi nazarin shawarwarin sun koka da cewa daftarin ya yi tsauri a wasu bangarorin a cewar Nicolas Reindrop na kungiyar agaji ta Oxfam dake Britaniya. Yace idan wannan shi ne tafarkin da gwamnatoci zasu bi domin cimma manufar shirin raya kasa na Millenium development goal, to kuwa sun fadi kasa wanwar domin kuwa ba zai ga ko ina ba. Shugaban babbar mashawartar majalisar Jean Ping na kasar Gabon ya baiyana cewa babu wani karfin zuciya da shugabannin kasashe masu arziki suka nuna na taimakawa kasashen Afrika kwatankwacin katafaren shirin nan na Marshal Plan da Amurka ta yi don taimakawa nahiyar turai farfadowa daga yakin duniya na biyu.

A dai daura da taron majalisar dikin duniyar manyan shugabanni na kasashe zasu yi ganawa da takwarorin su don tattauna batutuwa na diplomasiyya. Shugaban Amurka George W Bush zai gana da babban aminin sa Tony Blair na Britaniya wanda ya mara masa baya a yakin kasar Iraqi, bugu da kari zai tattauna shirin wanzar da zaman lafiya na gabas ta tsakiya da P/M Israila Ariel Sharon. A waje guda kuma sakataren majalisar dinkin duniyar Kofi Annan zai tattauna da shugaba George W Bush da Vladimir Putin na Rasha da Hu Jin tao na China da kuma P/M 50 na kasashe daban daban da suka hada da Tony Blair na Britaniya da Dominique de Villepin na Faransa da kuma Junichiro Koizumi na kasar Japan a yayin taron na kwanaki uku.