1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron kasa a Iraqi

March 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuPt

A ganawar su ta farko gaba da gaba tun bayan fara yakin Iraqi, jakadun Amurka dana Iran a taron yini guda don tabbatar da zaman lafiya a Iraqi, sun yi musayar yau inda kowanen su ke zargin juna da a game da tarzoma dake faruwa a kasar Iraqin. A jawabin sa P/M Iraqi Nuri al-Maliki ya roki dukkan mahalarta taron su taimakawa kasar sa fita daga kangin data sami kann ta a ciki da kuma hana rikicin yaduwa a fadin gabas ta tsakiya. Taron ya tafka muhawara a kann raáyoyin Amurka dana Iran a game da yadda zaá kawo karshen rikicin. Ministan harkokin wajen Iraqi Hoshiyar Zebari ya baiyana tattaunawa tsakanin kasashen Amurka da Britaniya, Iran da kuma Syria da cewa tana da matukar muhimmanci. Yayin da Amurka ta baiyana tura karin dakarun soji zuwa Iraqi, a hannu guda kuma tawagar kasar Iran tace matakin farko na samun zaman lafiya a Iraqi shi ne janyewar daukacin sojin Amurka dana sojin taron dangi daga kasar Iraqin. Tawagar mahalarta taron sun amince da sake haduwa a watan Aprilu. Manyan kasashe masu cigaban masanaántu G8 da suka hada da Jamus da Japan da Kanada da Italiya sun nuna shaáwar halaratar taron na gaba.