1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

250609 Islamkonferenz Schäuble

June 26, 2009

Ministan cikin gidan Jamus Wolfgang Schäuble ya nuna gamsuwa ga babban taron haɗin guiwa da wakilan musulmai a Jamus wanda aka kammala a jiya Alhamis bayan shekaru uku ana tuntuɓar juna.

https://p.dw.com/p/Ic44
Ministan cikin gidan Jamus Wolfgang SchaeubleHoto: AP

Ko da yake ba dukkan mahalarta taron ne ke da wannan ra´ayi ba, amma ɗaukacin mahalarta taron na masu ra´yin cewa ya kamata a ci-gaba da tattaunawar tsakanin Musulman da kuma gwamnati.

A kalamansa ministan harkokin cikin gidan na Jamus Wolfgang Schäuble ya gamsu da sakamakon babban taron da musulmi wanda shi ne ya ƙirƙiro da shi yana mai cewa musulmi wani ɓangare ne na al´umar Jamus. Ministan ɗan jam´iyar CDU ya bayyana wannan taron da ke zama irinsa na huɗu tun bayan fara shi a shekara ta 2006 da cewa ya taka muhimmiyar rawa ba ma a Jamus kaɗai ba a´a har da wajenta yana mai cewa taron ya samar da wani yanayi na amincewa da juna.

Ya ce: "Ko da yake dole ne a samu banbancin ra´ayi a wasu batutuwan amma burinmu shi ne samun kyakkyawan yanayin tattaunawa da juna tare da samun masalaha a a inda ra´ayi ya banbanta domin a ci-gaba da zama tare cikin lumana."

A dangane da haka ministan cikin gida yayi kira da a ƙara shigar da jihohi da ƙananan hukumomi a tarukan da za´a yi nan gaba. Ya ce da akwai matsaloli da dama da ya kamata a warware su musamman a fannin ba da ilimi. Ministan ya yi nuni da batun ɗaura ɗan kwali da darussan wasannin motsa jiki da koyar da dangantakar namiji da mace da kuma balaguro na ´yan makaranta.

Tun a cikin watan Maris na shekarar da ta gabata mahalarta taron suka amince da shigar darussan addinin musulunci a manhajar makarantun Jamus, amma bisa sharaɗi cewa za´a amince da addinin na musulunci a matsayin wata gamaiya ta addini a ƙasar, inji Schäuble.

Shi kuwa a nasa ɓangare shugaban majalisar ƙoli ta musulmi a Jamus, Ayyub Axel Köhler cewa yayi tuntuɓar junar da ake yi ta samar da kyakkywan sakamako a siyasance da kuma a tsarin zamantakewa. Saboda haka Köhler ya sa ran cewa za a ci-gaba da wannan tattaunawar tsakanin ƙungiyoyin musulmai daban daban da kuma sauran jami´an siyasa.

Ya ce: "Ina mai jaddada cewa an samu ci-gaba a shawarwarin da ake yi tsakanin ƙungiyoyin musulmai daban daban. Dukkan mun samu ƙarfin guiwa sakamakon babban taron na musulman Jamus."

Tun gabanin wannan zagaye na taron, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gayyaci mahalarta taron zuwa fadarta, inda ta amsa cewa ƙasar ta shafe shekaru masu yawa ba tare ta gudanar da shawarwari masu tsawo da musulmai ba. Ta yi nuni da cewa kamata yayi Jamus ta ba da la´akari da ƙasashen da musulman suka samo asali.

Ta ce: "Ko shakka babu ƙasar Turkiya na da muhimmiya ce a matsayin abokiyar shawararmu. Amma kuma mun san halin da ake ciki a ƙasashen Iran, Iraqi, Afghanistan, Pakistan, Libanon da kuma na yankin Arewacin Afirka. A ƙoƙarin sanin addinin musulunci muna ƙara fahimtar asalin ƙasashen da musulman a Jamus suka fito."

Alƙalumman baya bayan nan sun yi nuni da cewa yaawan musulmai a Jamus ya kai miliyan 4.3 waɗanda suka fito daga ƙasashe 49.

Mawallafa: Marcel Fürstenau/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Aliyu