Babban taron duniya akan AIDS a birnin Abuja | Labarai | DW | 04.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban taron duniya akan AIDS a birnin Abuja

Kwararrun masanan kiwon lafiya na Afirka da sauran kasashen duniya sun hallara a Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya don kaddamar da wani babban taro akan hanyoyi mafi dacewa wajen yakar cutar AIDS ko Sida a Afirka tare da kula da mutane miliyan 24 da cutar ta rutsa da su a wannan nahiya. In an jima da misalin karfe 5 agogon Nijeriya shugaba Olusegun Obasanjo zai bude babban taron karo na 14 akan cutar AIDS da sauran cututtuka dake yaduwa ta hanyar jima´i. Gabanin bikin bude taron, wakilai sun ce taron zai fi mayar da hankali akan yadda ya fi cancanta a kashe biliyoyin dala da gwamnatoci ke bayarwa don yaki da cutar da kuma yadda za´a hada kan ayyukan kungiyoyin agaji da ma´aikatun kiwon lafiya a Afirka da kungiyoyin addinai da kuma na kusa da jama´a.