Babban taro a Teheran game da nukiliya | Labarai | DW | 17.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban taro a Teheran game da nukiliya

A birninTeheran na ƙasar Iran an buɗa babban taro game da nukiliya daura da na Washington

default

Taron Teheran game da nukiliya

Yau ne aka buɗa babban taro game da nukiliya a ƙasar Iran, bisa jagorancin shugaba Mahmud Ahmadinedjad.Ministocin harakokin wajen ƙasashen Syria, Iraqi da Libanon dake halartar taron,sun nuna goyon baya ga shirin nukiliyar Iran, da suka ce na lumana ne. Ministocin sun kuma buƙaci Isra'ila ta sanya hannu kan yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya ba tare da gindaya wasu sharuɗɗa ba.

Sannan sun yi watsi da takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya bisa matsin lambar Amurika ta ƙaƙabawa Iran.

A lokacin da yake jawabi a taron, mataimakin ministan harakokin wajen Rasha Sergei Rjabkow cewa yayi:

" Hukunci akasari bashi da wani tasiri, saidai a wani lokacin, cilas ce ke sawa a ɗauki irin wannan mataki.Zamu iya namu ƙoƙari, domin warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar tattanawa."

Kafofin sadarwa a Iran, sun ce wakilai daga ƙasashe kimanin 60  ke halartar taron, wanda ke matsayin  daura da babban taron ƙasashe 47 da shugaba Barak Obama ya kira a Washington a farkon wannan mako.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Abdullahi Tanko Bala