1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya buɗe wani taro kan yankin Darfur a Addis Ababa .

November 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bubh

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya buɗe wani taron ƙasa da ƙasa kan yankin Darfur a birnin Addis Ababa. Mahalarta taron sun haɗa ne da wakilai daga ƙasashen Larabawa da na nahiyar Turai da kuma Afirkan da kanta, inda za su yi yunƙurin samo bakin zaren warware rikicin tashe-tashen hankullan da ke ta ƙara taɓarɓare al’amura a yankin na Darfur, na ƙasar Sudan. Annan dai ya ce yana son ganin dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, sun maye guraban takwarorinsu na Ƙungiyar Tarayyar Afirka a yankin, kuma yana son ganin hakan ya wakana ne kafin ya sauka daga muƙaminsa a farkon watan Janairu na shekara mai zuwa. Amma kawo yanzu, Sudan na biris ne da kiran da gamayyar ƙasa da ƙasa ke yi mata na ta amince da girke dakarun Majalisar Ɗinkin Duniyar a yankin na Darfur.

Taron dai ya kuma sami halartar jami’ai daga Ƙungiyar tarayyar Afirka, da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, da Sudan ɗin da kanta, da Amirka, da Sin, da Rasha, da Masar, da Faransa da sauran wasu ƙasashe na nahiyar Afirka.