1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban Sakataren Ƙungiyar Musulmi ta Duniya zai ziyarci Iran don tattauna batun makamashin nukiliyan ƙasar.

May 29, 2006
https://p.dw.com/p/BuwE

Ƙungiyar Musulmi Ta Duniya, ta ba da wata sanarwa yau a birnin Jeddah, cewa Babban Sakatarenta, Ekmeleddin Ihsanoglu, zai kai ziyara a birnin Teheran a ran laraba mai zuwa, inda zai yunƙuri cim ma sassaucin tsamari a ce-ce-ku-cen da ake yi kan batun makamashin nukiliyan Iran. Sanarwar ta ƙara da cewa, babban sakataren zai tattauna da mahukuntan Iran ne kan irin rawar da Ƙungiyar za ta iya takawa, wajen cim ma madafa a rikicin da ake yi a halin yanzu kan batun makamashin nukiliyan.

Ita dai Ƙungiyar Musulmi Ta Duniyar, mai hedkwatarta a ƙasar Saudiyya, tana goyon bayan warware matsalar ne ta hanyar diplomasiyya. Amma kuma, inji sanarwar, tana kan matsayinta ne na goyon bayan ’yancin ko wace ƙasa ta yi amfani da makamashin nukiliyan ta hannunka mai sanda.

Iran dai ta dage ne kan cewar, shirin makamshin nukiliyanta, wato wani tanadi ne na tabbatar wa kanta isashen makamashi nan gaba. Amma ƙasashen Yamma na ta angaza mata, da ta soke duk wasu shirye-shirye na sarrafa Yureniyun, abin da suke gani kamar zai bai wa Iran ɗin damar ƙera makaman ƙare dangi.