1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban kotun ƙasar Jamus, ta sami ɗan ƙasar Marokon nan, Al—Motassadeq da laifin taimaka wa masu kisan gillla.

November 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bubq

Kotun ƙoli ta tarayya ta nan Jamus, ta sami ɗan ƙasar Marokon nan da ake yi masa shari’a, da laifin tallafa wa ’yan ta’adda wajen kai hare-haren ƙunan bakin wake da kisan gilla, dangane da harin ƙunan bakin waken nan da aka kai a ran 11 ga watan Satumba qa biranen New York da Washington a Amirka.

Wannan shawarar da kotun ta yanke dai, ya sa ke nan za a sake buɗe shari’ar Motassadeq ɗin a kotun da ta fara yanke masa hukunci, kafin ya ɗaukaka ƙara. A cikin watan Agustan shekarar bara ne wata kotu a birnin Hamburg ta yanke wa ɗan kasar Marokon, mai shekaru 32 da haihuwa, hukuncin dauri na shekaru 7 a gidan yari, bayan ta same shi da laifin kasancewa ɗan wata ƙungiyar ’yan ta’adda. A shekara ta 2003 kuma, an yanke wa Motassadeq ɗin hukuncin ɗauri a gidan yari na shekaru 15, saboda laifin da ake zarginsa da shi na samun hannu a kisan gillar da aka yi wa fiye da mutane dubu 3 a Amirkan. Sai dai kotun ɗaukaka ƙara ta soke wannan hukuncin, saboda ba a sami hujjojin da ake bukata daga shaidu ba.