Babban Kommandan Rundunonin Amurika ya ziyarci Ethiopia | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban Kommandan Rundunonin Amurika ya ziyarci Ethiopia

Shugaban rundunar tarayya ta dakarun Amurika Jannar John Abizaid, ya tantana da hukumomin Ethiopia a game da halin da ake ciki, a yankin gabancin Afrika, ta fannin yaki da ta´danci.

Kazalika Jannar Abizaid, ya tanatana da Praminista Meles Zenawi a game da harokoin diplomatia tsakanin Amurika da Ethioia.

A dazunan ,ya bar Addis Ababa, zuwa sansanin sojojin Amurika da ke kasar Djiboutie.

Kasashen 2, na da kyaukyawar dangantaka, ta fannin yaki da ta´danci, mussamman bayan zargin da Amurika tayi wa kotunan musuluncin Somalia mai makwabtaka da Ethiopia, na boye membobin kungiyar Alqa´ida.