Babban Jami´in diplomasiyan EU Solana zai kai ziyara a Teheran | Labarai | DW | 03.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban Jami´in diplomasiyan EU Solana zai kai ziyara a Teheran

Wani labarin da ya iso mana yanzu na cewa babban jami´in na kungiyar EU ka iya kai ziyara birnin Teheran a wani mataki na shawo kan hukumomin kasar su amince da jerin taimakon da aka alkawarta musu. A gobe lahadi mista Solana zai fara rangadin yaankin GTT, inda zai gana da jami´an Isra´ila da na Falasdinawa, amma kakakinsa ya fadawa kamfanonin dillancin labaru a birnin Brussels cewa ana iya canza ajandar tafiyar don bawa Solana din damar yada zango a Teheran.