1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban gangami na 'yan adawa a Kwango

Saley / Mouhamadou A.Balarabe/ SBAugust 1, 2016

A wani taron gangami da ya shirya, madugun 'yan adawan Kwango Etienne Tshisekedi ya nemi gwamnati da ta shirya zaben shugaban kasa kafin karshen wannan shekarar.

https://p.dw.com/p/1JZn1
Kongo Demonstration der Opposition in Kinshasa
Taron 'yan adawan kasar Kwango a birnin KinshasaHoto: Getty Images/AFP/E. Soteras

Dubban magoyan bayan Tshisekedi ne suka halarci gangamin da gamayyar jam'iyyun adawan Kwango ta shirya a birnin Kinshasa domin sauraron jawabin madugun 'yan adawa. Dama dai rabon da ya yi jawabi a bainan jama'a tun shekara ta 2011, lokacin da aka gudanar da zaben shugaban kasa na karshe.

Ko da shi ke ya samu goyon bayan sauran shugabannin adawa, amma kuma shugaban jam'iyyar UDPS da ta samu karbuwa a Kwango ya zama ja gaba wajen nuna shakku kan shirya zaben shugaban kasa a karshen 2016. Hasali ma dai, 'yan adawa na ganin cewar shugaba Joseph Kabila, wanda wa'adinsa zai kare a ranar 20 ga watan Disemba, na son yin amfani da karfin ikonsa wajen ci gaba da rike madafun iko, lamarin da Tshisekedi ya ce ba za ta sabu ba.

Kongos Tschisekedi ist nach Kinshasa zurückgekehrt
Madugun 'yan adawan kasar Kwango Etienne Tshisekedi ya yin da zai koma a kasarsa ta KwangoHoto: picture-alliance/AP Photo/P Photo/J. Bompengo

"Ranar 19 ga watan satumba, rana ce da bai kamata a tsallake ba, ba tare da sanar da jadawalin zaben shugaban kasa ba. Idan ba a dauki wannan mataki ba, zai zama wani cin amanar kasa daga shugaba kabila wanda alhakin mummunan halin da 'yan Kwango suke ciki ya rataya a wuyan shi."

Tshisekedi ya nemi a sako Katumbi kafin a tattauna

Madagun 'yan adawan na Kwango, ya kuma bayyana cewar kofarsa a bude take ga duk wata tattaunawa da gwamnati kan lamarun siyada da ci gaban kasa. Sai dai ya ce zai hau kan teburin tattaunawar ne bisa wasu sharudda, ciki kuwa har da sako duk 'yan adawa da ke tsare. Dama dai Moise katumbi tsohon abokin burmin Kabila da ya koma bangaren adawa ya zargi gwamnati da yi masa bita da kullin siyasa. Kotu ta yanke masa hukuncin shekaru uku a gidan yari bayan da ta sameshi da laifin amfani da sojojin haya da suka zo daga Amirka, lamarin da ya karyata.

Sai dai dan majlisa Gregoire Lusenge, wanda yake sahun farko na wadanda ke neman taka wa kabila birki ta ko halin kaka a yunkurinsa na tazarce ya ce 'yan Kwango sun bayyana alkiblar da suke so kasarsu ta dosa.

"Wannan gangamin da aka shirya ya bai wa kasashen duniya damar fahimtar cewar 'yan Kwango da suka amsa kiran da 'yan adawa suka yi musu na neman sauyi"

Tun a watan Nuwamban na 2015, shugaba kabila ya shirya tattaunawa da nufin kauce wa tashe-tashen hankula a lokacin zabe. Madagun 'yan adawan Kwango na daga cikin 'yan siyasa da suka amince za su shiga a dama da su. Sai dai a yanzu Etienne Tshisekedi ya zargi Edem Kodjo wanda Kungiyar Gamayyar Afirka ta nada don shiga tsakani a tattaunawar da goyon bayan bangaren Kabila.

Kongo Demonstration der Opposition in Kinshasa
babban taron gangamin 'yan adawan kasar KwangoHoto: Getty Images/AFP/E. Soteras

Shi ma Junior Moutala mai shekaru 21 wanda kuma ke goyon bayanTshisekedi ya ce tattaunawar ta kama hanyar rikida zuwa taron nuna goyon baya ga tazarcen Kabila.

"Mun jima muna tattaunawa ba tare da samun ci gaba ba. A yau mun fahimci cewa sai idan an aurari koke-koken al'umma ne kwalliya za ta biya kudin sabulu. Saboda shugaba Kabila ya gane cewar ba mu zabe shi bisa dokokin zaman tattaunawa ba, amma bisa ga kundin tsarin mulki."

Etienne Tshisekedi mai shekaru 83 da haihuwa tsohon jemage ne a fagen siyasar Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, saboda baya ga Mobutu SeseSeko, ya kuma kara da Laurent-Désiré kabila tsohon shugaban kasa kana mahaifin shugaban Joseph kabila mai ci yanzu. Shi Tshisekedin ne ma ya zo a matsayi na biyu a zaben shugaban kasa na 2011 wanda ya yi watsi da sakamakon da aka bayyana.