1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban alkali a shari´ar da ake yiwa Saddam Hussein zai yi murabus

Babban alkalin da ke shugabantar zaman sauraron shari´ar da ake yiwa tsohon shugaban Iraqi Saddam Husein ya mika takardun yin murabus. Wani na kurkusa da shi ya ce alkali Rizgar Mohammed Amin ya nuna rashin jin dadinsa ne game da korafe korafen da jama´a da ma gwamnatin Iraqi ke yi a dangane da yadda shari´ar ke gudana. A can baya dai kafofin yada labarun Iraqi sun yi zargin cewa alkali Amin ya rasa makama a shari´a sannan kuma yana yiwa Saddam Hussein sassauci. A ranar 24 ga watannan na janeru za´a koma zaman sauraron shari´ar. A halin da ake ciki jami´ai a kotun na kokarin shawo kan alkalin don ya janye takardun yin murabus din.