1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babba taron masu ba da taimako a Pakistan

November 19, 2005
https://p.dw.com/p/BvKU
Nelson Mandela, tsohon shugaban Afirka Ta Kudu.
Nelson Mandela, tsohon shugaban Afirka Ta Kudu.Hoto: AP

An bude wani babban taron kasashe masu ba da taimako a Pakistan a wani yunkuri na tara biliyoyin daloli da Pakistan din ke bukata don sake farfado da yankin da mummunar girgizar kasar nan ta watan jiya ta yi kaca-kaca. A lokacin da yake bude zaman taron na yini daya a birnin Islamabad, FM Pakistan Shaukat Aziz ya ce da akwai matukar bukatar yin wani abu cikin gaggawa. Girgizar kasar ta halaka mutane kusan dubu 74 yayin da mutane miliyan 3.5 suka rasa muhallinsu. A cikin jawabin sa babban sakataren MDD Kofi Annan ya ce taimakon da kasashen duniya suka bayar kawo yanzu bai wadatar ba. Annan ya ce Pakistan ta samu kashi 30 cikin 100 kadai na agajin da ta ke bukata don sake gina yankunan da girgizar kasar ta yiwa barna.