Ba´a samu kusantar juna ba tsakanin EU da Iran | Labarai | DW | 11.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba´a samu kusantar juna ba tsakanin EU da Iran

An kammala shawarwari tsakanin KTT da Iran game da shirinta na nukiliya ba tare da cimma wata yarjejeniya ta kusantar juna ba. Bayan ganawar da yayi da babban jami´in diplomasiyar KTT a birnin Brussels, shugaban tawaragar Iran a tattaunawar da ake yi game da shirinta na nukiliya Ali Larijani ya nunar da cewa kasar sa na bukatar karin lokaci kafin ta mayar da jawabi akan tayin taimakon da kasashe biyar masu ikon hawa kujerar naki a kwamitin sulhun MDD da kuma Jamus suka ba ta. Ganawar ta yau ta mayar da hankali ne akan tayin taimakon wanda aka bayar da nufin gano bakin zaren warware wannan takaddama. Tayin ya tanadi bawa Iran taimakon tattalin arziki da na siyasa idan kasar ta yi watsi da shirin ta na inganta sidanarin uranium. Tun da farko Iran ta nunar da cewa a cikin watan augusta zata ba da amsa ga wannan shawara.