1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba´a kawad da yiwuwar sanyawa Iran takunkumi ba

January 28, 2006
https://p.dw.com/p/BvAV
Tare da amfani da kalamai masu tsauri a karon farko ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier yayi barazanar kakabawa Iran takunkuman karya tattalin arziki idan kasar ta ki ba da hadin kai don warware rikicin nukiliyar ta a hanyoyin diplomasiya. A lokacin da yake hira da mujallar Spiegel ministan ya ce bai kamata Iran ta raina irin dogaron da take yi akan hadin kan fasaha da tattalin arziki da kasashen yamma ba. A yau asabar Steinmeier zai gana da daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Mohammad El-Baradei a birnin Vienna. Shi kuwa a nasa bangaren sakataren harkokin wajen Birtaniya Jack Straw ya ce har yanzu kofa a bude take wajen warware wannan takaddama da Iran ta hanyar diplomasiya. A lokacin da yake magana a gun taro kan tattalin arzikin duniya a Davos na kasar Switzerland mista Straw ya ce dole ne kasashen yamma su cimma wata matsaya guda wadda dukkan sassan biyu zasu yi maraba da ita.