1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba zaá tura Yarima Harry cikin dakarun soji zuwa Iraqi ba

May 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuLO

Maíkatar tsaron Britaniya ta sanar da cewa ba zaá tura Yarima Harry a cikin ayarin sojojin da zaá tura zuwa Iraqi ba. Babban hafsan sojin Britaniya janar Sir Richard Dannat ya shaidawa yan jarida cewa rundunar sojin Britaniya ta fahimci cewa akwai haɗari da kuma barazana mai yawa da sojojin za su fuskanta idan aka tura shi zuwa Iraqin. Janar Dannat yace sakamakon ziyarar da ya kai Iraqi, ya gano cewa akwai gagarumin kalubale na hare hare da yan takife ke shirin kaiwa ga rundunar da Harry zai jagoranta da ma kuma yunƙurin yin garkuwa da shi kan sa Yariman. Yace ya fahimci cewa Yarima Harry ba zai ji daɗin wannan matakin ba, amma abu ne da ya zama wajibi. Babban hafsan sojin ya kuma jinjinawa Harima Harry bisa kishi da kuma jaruntakar da ya nuna.