Ba tantama yunwa a Arewa maso Gabashin Najeriya | Siyasa | DW | 15.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ba tantama yunwa a Arewa maso Gabashin Najeriya

Gwamnati da hukumomin agaji sun amince da cewa akwai wannan matsala ta karancin abinci tsakanin 'yan gudun hijira kusan miliyan biyu da ke zaune a cikin al'umma inda su ka ce yanzu nan ne za su fi maida hankali.

Miliyoyin mutane a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya na fama da matsalar yunwa karancin abinci, abin da ake alakantawa da rikicin Boko Haram da ya hana mutane noma da sauran harkokin neman abinci musamman tsakanin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.

Wani rahoton Malajisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kimanin mutane miliyan 10 ake fargabar suna fuskantar matsananciyar yunwa a Najeriya kuma mafi yawansu sun fito daga shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya inda rikicin Boko Haram ya daidaita.

Sama da mutane miliyan biyu ne hukumomi suka tabbatar da su na zaune a Maiduguri bayan da rikicin Boko Haram ya raba su da matsugunansu kuma yawanci ke zama cikin al'umma wajen 'yan uwa da abokan arziki. Da yawansu ba su samu yin noma da aka san mutanen yankin da yi ba, abin da ya sa dole siyar da kayayyakinsu domin sayen abinci inda komai na hanunsu ya kare suka koma yin barace-barace.
 

Wasu daga cikin irin wadannan 'yan gudun hijira sun bayyana halin da suke ciki a tsawon zamansu bayan tserewa daga matsugunansu, halin kuma ba mai sauki ba ne a cewarsu. Gwamnati da hukumomin agaji sun amince da cewa akwai wannan matsala ta karancin abinci tsakanin 'yan gudun hijirar kusan miliyan biyu da ke zaune a cikin al'umma inda su ka ce yanzu nan ne za su fi mayar da hankali.

Gwamnman jihar Borno ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa 'yan gudun hijira da ke zaune a tsakanin 'yan uwansu su ne babbar matsalar ayyukan agaji a yanzu haka. Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno Injniya Ahmad Satomi ya tabbatar da matsayin gwamnati kan miliyoyin wadanda suke fuskantar matsalar yunwa a Maiduguri.

Akwai dubban mutane da yanzu haka yaki da ake yi tsakanin sojojin da Boko Haram ya rutsa da su ba sa iya samun abinci ko ruwan sha kuma ba za su iya ficewa ba saboda yadda ake gwabza fada a yankin.

Haka za lika duk da cewa an samu albarkatun noma a wasu sassan Arewa maso Gabashin Najeriya yadda abinci ya yi tsada ya sa wasu ba sa iya siyen abinci, lamarin da ya kara tsananta barazanar da yunwa ke yi wanda ake gani in ba a dauki mataki ba miliyoyin ka iya mutuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin