Ba ta kashi tsakanin Hamas da Fatah | Labarai | DW | 22.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba ta kashi tsakanin Hamas da Fatah

Duk da yarjejeniyar sulhu, da aka ratabawa hannu, tsakanin ƙungiyoyin Hamas da na Fatah, har yanzu ƙura ba ta laffa ba azirin Gaza, a gumurzun da ɓangarorin 2 ke fama da shi.

A yamacin jiya , wasu yan takife Hamas, sun kai hari ga Mohamed Chahada,ɗaya daga jami´an da ke kula da tsaron lahiyar shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas.

Jami´in ya ƙone cikin motar sa, da yan Hamas ɗin, su ka bamkawa wuta a tsakiyar Gaza.

Wannan hari ya wakana kwana 2 bayan wanda ya a kaiwa ayarin motocin Praminista Isma´il Hanniey.

Rikicin tsakanin Hamas da Fatah ya barke tun watan Janairu, na wannan shekara, bayan, da Hamas ata yi nasara, a zaɓen yan majalisun dokoki.