Ba isassun abubuwan kare lafiya a cikin jirgin ruwan Masar | Labarai | DW | 05.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba isassun abubuwan kare lafiya a cikin jirgin ruwan Masar

Wadanda suka tsira daga mummunan hadarin jirgin ruwan nan da ya auku a tekun Bahar Maliya sun yi zargi game da rashin isasshen tanadin abubuwan kare lafiyar fasinjoji a cikin jirgin. Suka ce ba isassun rigunan tsira da kwale-kwalen fita daga jirgin cikin gaggawa lokacin da jirgin ruwan ya fara nitsewa sakamakon wata gobara da ta tashi. A jiya arangama tsakanin dangi wadanda hadarin ya rutsa da su da ´yan sanda a tashar jirgin ruwa ta Safaga dake Masar. An yi ta jifar ´yan sanda da duwatsu lokacin da tarzomar ta barke. Su kuma a nasu bangare ´yan sanda sun yi amfani da kulake da barkonon tsohuwa don kwantar da tarzomar. Hukumomi sun ce mutane 350 daga cikin fasinjoji dubu 1400 suka tsira daga wannan bala´i.