Ba bu alamar lafawar rikicin a fadin kasar Iraki | Labarai | DW | 31.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba bu alamar lafawar rikicin a fadin kasar Iraki

Sabon FM Iraqi Nouri al-Maliki ya kai ziyara a birnin Basra cibiyar samar da man fetir dake kudancin Iraqin, inda ake fama da dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin ´yan shi´a da basa ga maciji da juna, wadanda ke gwagwarmayar rike madafun iko. Maliki ya gana da jami´ai da kuma shugabannin kabilun yankin, inda yayi barazanar yin amfani da karfi akan abin da ya kira kungiyoyin ´yan banga. Rahotannin da ke iso mana daga birnin Bagadaza kuma na cewa an gano gawawwaki 42 a wurare daban daban na wannan birni. ´Yan sanda sun ce wasunsu na dauke da raunukan harbin bindiga da kuma azabtarwa. Sannan wani harin bam da aka kai da mota a birnin Mosul dake arewacin kasar ya halaka ´yan sanda biyar. Hare haren bama-bamai da aka kai jiya talata a Bagadaza da kuma Hilla sun yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 53 yayin 65 suka jikata. A kuma halin da ake ciki gwamnatin Amirka ta tabbatar da cewa zata buga rahoton sakamakon binciken da ake gudanarwa akan zargin cewa sojojin ta sun yiwa fararen hular Iraqi su 24 kisan gilla a garin Haditha cikin watan nuwamban bara.