1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba alamar cimma tudun dafawa a taron kungiyar WTO

December 17, 2005
https://p.dw.com/p/BvG2

Tare da muhawwara game da sanya lokacin da za´a soke dukkan tallafin da ake ba wa kayan albarkatun noma da ake aikawa ketare, babban taron kungiyar cinikaiya ta duniya WTO ya shiga zagaye na karshe. Kwamishinan ciniki na kungiyar tarayyar Turai Peter Mandelson ya nuna shirin tattaunawa akan soke tallafin bayan shekara ta 2013. Mandelson ya ce tarayyar Turai ba zata amince da shawarar da aka gabatar da farko na soke kudaden tallafin a shekara ta 2010 ba. A lokaci daya kuma kwamishinan ciniki ya yi suka game da daftarin sanarwar bayan taro da sakatare janar na kungiyar WTO Pascal Lamy ya gabatar da cewa ko kadan bai wadatar ba. Ita ma tarayyar Jamus ta yi watsi da muhimman batutuwan dake kunshe cikin daftarin wato game da kayan masana´antu da aikin yiwa jama´a hidima da cewa ba abin karbuwa ba ne. Daftarin sanarwar bayan taron ya tanadi soke tallafin da ake bawa manoman auduga daga shekara ta 2006.