Ba alaman nasara a tattauna rikicin Siriya | Labarai | DW | 23.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba alaman nasara a tattauna rikicin Siriya

 A yau ne aka fara wani zagayen tattauna rikicin kasar a Geneva to amma bisa bayanan da aka samu a ranar farko akwai babban gibi tsakanin bangarorin masu gaba musamman tsauraran sharrudan 'yan tawaye

Inda Manzon MDD kan rikicin Sirya Steffan de Mistura ya ce "Ban son ko lokaci ya yi na kulla yarjejeniyar diddin tsakani masu fada da juna ba, amma dai lokaci ya yi na fara sasantawa. Domin ana aiwatar da tsagaita wuta, na biyu kuma akwai dama a yanzu da za'a iya yin sauri a dau mataki" A gefe gudawa kuwa a kasar ta Siriya an gano wani katon rami dauke da kimanin gawakin mutane 130 wadanda kungiyar IS ce aka tuhama da yi musu kisan gilla. Rahotannin suka ce an gano gawakinne a yankin Idlib, inda kungiyoyin 'yan ta'addan ke fafatawa bayan baraka da aka samu tsakaninsu. Ko da a makon jiya an samu wani ramin da aka binne mutane 41 a birnin.