baƙin haure da dama sun mutu a hanyar su ta tsibirin Canarie domin shiga turai | Labarai | DW | 27.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

baƙin haure da dama sun mutu a hanyar su ta tsibirin Canarie domin shiga turai

Rahotani daga opishin tsaro na Mauritania sun ce, a ƙalla mutane 14 su ka nutse cikin ruwan teku, sannan an ceto kimanin mutane 180, a yunkurin su na shiga turai ta hanyar tsibirnin canarie na ƙasar Spain.

Mutanen sun hito daga gaɓar tekun Senegal.

Daga farkon wannan shekara zuwa yanzu ,kussan mutane dubu 20 ,su ka bukaci anfani da tsibirin Canarie, domin shiga turai ba tare da cimma buri, ma.

Ƙasashen Spain da Senegal, sun cimma yarjejeniyar gama ƙarfi, domin yaƙi da kwararar baƙin haure, daga ƙasashen Afrika zuwa turai, ta ɓarauniyar hanya