Baƙin haure 250 sun isa a tsibirin Canaries na Spain. | Labarai | DW | 23.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baƙin haure 250 sun isa a tsibirin Canaries na Spain.

Jami’an tsaron iyakokin gaɓar tekun ƙasar Spain, sun ce sun kame ƙananan kwale-kwale guda 4, ɗauke da baƙin haure daga Afirka Ta Yamma, yayin da suke yunƙurin isa kan tsibirin nan na Canaries. Wata sanarwar ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta ce, wasu daga cikin baƙin hauren sun galabaita saboda rashin ruwa, kuma ana yi musu jiyya a asibiti. Tun farkon wannan shekarar dai, kusan ɓakin haure dubu 10 daga Afirka Ta Yamman ne suka ɗau kasadar yin ƙaura cikin ƙananan kwale-kwale zuwa Turai, inda a lokuta da dama, suke nitsewa cikin teku kafin su cim ma burinsu.