Baƙin haure ɗari 2 da 50 sun isa a tsibirin Canaries. | Labarai | DW | 31.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baƙin haure ɗari 2 da 50 sun isa a tsibirin Canaries.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar Spain, ta ba da sanarwar cewa, jami’an tsaron iyakar ƙasar sun kame wasu ƙananan jiragen ruwa guda uku, ɗauke da baƙin haure sama da ɗari 2 da 50 daga nahiyar Afirka, waɗanda ke yunƙurin sulalawa zuwa tsibirin Canaries.

Rahotanni dai sun ce baƙin haure fiye da dubu 19 ne suka kutsa zuwa tsibiran Spain ɗin a wannan shekarar, abin da ya ninka yawansu har sau 4, idan aka kwatanta adadin shekarar bara. Gwamnatin Spain ɗin da kanta kuma, ta ce a cikin wannna watan Agusta kawai, yawan baƙin hauren da suka shigo ƙasar ya fi na duk shekara ta 2005. Yau ne dai ministan harkokin cikin gidan ƙasar, Alfredo Perez Rubalcaba, zai bayyana wa majalisa irin matakan da gwamnatin Spain ɗin za ta ɗauka don magance ambaliyar baƙin hauren. A cikin matakan kuwa, har da sintirin rukunan rundunar mayakan ruwan ƙasar a kan teku, tare da takwarorinsu daga Senegal da Murteniya, ƙasashen da baƙin hauren ke taruwa kafin su ɗau kasadar kutsawa zuwa Spain ɗin. Mataimakiyar Firamiyan ƙasar, Maria Teresa Fernandez, ta ziyarci birnin Brussels don bayyana wa jami’an Ƙungiyar Haɗin Kan Turai cewa, wannan matsalar dai matsalar ƙungiyar ce gaba ɗaya, amma ba ta Spain kawai ba.