1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Baƙi ´yan kasuwa a Jamus na ƙara kakkafa kamfanonin kansu

Harkokin Kasuwanci a Trayyar Jamus

default

Kasuwar kayan lambu a Bonn

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Mu Kewaya Turai, shirin da ke kawo muku batutuwan da suka shafi siyasa, tattalin arziki, al´adu, zamantakewa da kuma dangantaka tsakanin ƙasashen nahiyar Turai.

Alƙalumma sun yi nuni da cewa a nan Jamus akwai kamfanoni daga ƙanana har izuwa manyan dubu 300 mallakin baƙi waɗanda suka yi kaƙa-gida cikin ƙasar. To sai dai idan Jamusawa na magana game da baƙi ´yan kasuwa a cikin ƙasar hankalin ya fi karkata ga wuraren sayar da abinci na kan hanya musamman na Turkawa da kantunan da shagunan buga waya da sayar da wayoyin salula da kantunan sayar da kayan abinci na baƙi. To ko shin haka abin ya ke a zihiri? Shirin Mu Kewaya Turai na wannan mako zai yi tsokaci ne a kan wannan batu. Masu sauraron Mohammad Nasiru Auwal ke marhabin da saduwa da ku a wannan lokaci.

Rene Leicht na cibiyar nazarin hada-hadar matsakaitan kamfanoni a jami´ar birnin Mannheim, ya shafe shekaru masu yawa yana gudanar da bincike kan kamfanonin baƙi a nan Jamus, yayi bayani yana mai cewa.

“Kusan a ce da ƙanshin gaskiya cikin wannan batu, to amma a wani lokacin a kan yi ƙarin gishiri, domin hankalin jama´a ya fi karkata ga abin da ya ke a bayyane, musamman shaguna da kantuna dake gefen hanya. To amma ofisoshi da ƙananan wuraren sana´o´i da ke cikin harabobin gidaje waɗanda ba safai ne ɗaukar hankalin mutane ba.”

An yi ƙiyasin cewa kusan kashi ɗaya cikin biyar na mazauna a nan Jamus sun yi ƙaura ne zuwa ƙasar ko kuma iyayen su baƙi ne ´yan ƙaƙa-gida. A cikin shekarun baya bayan nan yawan mutanen da suka kafa wuraren sana´o´in kan su a tsakanin wannan rukuni na mazauna Jamus ya ƙaru ƙwarai da gaske. Yanzu haka dai alƙalumma sun nunar da cewa kashi ɗaya bisa goma na kamfanoni a nan Jamus, baƙi waɗanda ba su da asali da Jamus ke kafawa. Inji Holger Hey shugaban ƙungiyar masana´antu da kamfanoni na Turkawa da Jamusawa, sannan sai ya ƙara da cewa.

“Irin waɗannan kamfanoni da baƙi ke kafawa suna da fannoni daban daban kuma suna tafiya da sauyin zamani. Gudunmawar da suke bayarwa kuwa ba kaɗan ba ce.”

Tun a cikin shekarun 1990 yawan baki dake kafa kamfanonin kansu ya ninka fiye da sau biyu. Hakan dai na da dalilai guda biyu. Na farko shi ne a tsakani baƙin ana samu canji na zamani. Alal misali a lokacin da rukunin iyayen bakin suka shigo Jamus a shekarun 1960 zuwa 1970, sun shigo kasar ne a matsayin baƙi ´yan ci-rani, inda aka ɗauke su aiki a manyan kamfanoni. To yanzu ´ya´ya da jikokinsu ne ke neman wata hanya ta daban don samun halaliyarsu. Na biyu kuma shi ne da yawa daga cikin baƙin ba sa samun aikin yi sakamakon matsalar yawan marasa aikin yi a nan Jamus kuma ganin cewa ba zasu iya gogayya da takwarorinsu Jamusawa wajen nema ko samun aiki ba, to hanya ɗaya tilo ta magance wannan matsala ga baƙin shi ne kafa wuraren sana´o´i ko kananan kamfanoni kansu don samun abin sakawa bakin salati.

Daga cikin baƙin da ke kakkafa kamfanonin kansu, Turkawa da Jamusawa ´yan asalin ƙasar Turkiya sun fi yawa. To sai dai tun ´yan shekaru kaɗan da suka gabata, ´yan ƙasar Poland ma sun shiga jerin baƙi dake samawa kansu aikin yi. To amma ga Rene Leicht na cibiyar nazarin hada-hadar matsakaitan kamfanoni a jami´ar birnin Mannheim wannan wani lamari ne na daban.

“Dalilin da ya sa suke zaɓen wannan hanya shi ne da yake a nan Jamus ba a fara ba su izinin kafa kamfanoni balantana ma su dauki wani aiki ba, saboda haka suke kafa kamfanoni masu zaman kansu amma na boge, inda su ke tafiyar da aiki na hadin guiwa musamman a kamfanonin gine-gine.”

Fannin da baƙin ko Jamusawa masu asali da kasashen waje da suka fi yawa a ciki shi ne na wuraren sayar da abinci, wanda yanzu yawan su ya kai kashi 50 cikin 100 na dukkan kamfanoni dake a nan Jamus. A wannan fannin kuwa bakin na taka muhimmiyar rawa wajen yada al´adunsu da nuna ƙwarewa wajen dafa abinci irin na ƙasashensu. Alal misali ´yan asalin Girika sun fi ƙwarewa wajen soya nama da ake hadawa da albasa da madara, sannan ´yan Italiya sun yi suna wajen gasa Pizza yayin da ´yan China kuma suke nuna hazaƙa wajen mulmula da soya wani burudi da ake sa kayan lambu a cikinsa.

“A halin da ake ciki masu kakkafa kamfanoni sun fi mayar da hankalinsu akan kasuwannin ga baki daya, kuma da yawa daga cikin abokanen huldar cinikinsu Jamusawa ne. Wato yanzu haka dai an fita daga zamanin nan na yin hulɗar kasuwanci da ´yan asalin ƙasar ka kaɗai an shiga sabon yayi na samar da kayayyaki iri daban daban ga kasuwar baki ɗayan ta.”

Wadannan nan dai kalaman Jengiz Yildirim ne mai binciken kimiyya na cibiyar nazarin al´adun Turkawa dake birnin Essen. Ya ce Turkawa da sauran baki masu kamfanoni suna taka muhimmiyar rawa ba kawai wajen cike kasuwanni da kayan abinci ba, a´a suna kuma ba da gudunmawa a fannin yiwa jama´a hidima kamar aikin lauya, bawa kamfanoni shawara da aikin likita. Ban da ƙwarewar a sana´o´insu daban daban suna da kuma wata fa´ida ta musamman. Wato sun iya yarurruka daban daban kana kuma sun san al´adun Jamusawa da na ƙasashensu na asali. Hakan ganau ne ba jiyau ba musamman ga Jamusawa da kuma baƙin su kansu, inji Jengiz Yildririm sannan sai ya ƙara da cewa.

“Mutanen da suka samarwa kansu wani matsayi a fannin tafiyar kyakkyawar hulɗar kasuwanci na nuni da cewa su ma wani ɓangare ne na al´umar wannan ƙasa waɗanda suka dauki nauyin kansu da kansu. Wato kenan ana bukatar wani kyakkyawan zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka kafin zamantakewa tsakanin al´umomi ta yi kyau.”