1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

180809 Dialog Ramadan Deutschland

August 28, 2009

shirin na wannan karon zai mayar da hankali ne akan azumin watan Ramadana a nan Jamus.

https://p.dw.com/p/JJon
Ba da abincin buɗe baki kyauta ga musulmi da waɗanda ba musulmi ba a birnin Essen na nan JamusHoto: picture-alliance/ dpa

A ƙarshen mako ne al´umar musulmi a ko-ina cikin duniya suka fara azumin watan Ramadana, ɗaya daga cikin shika-shikan addinin musulunci guda biyar. Ga musulmai mazauna nan Jamus azumin na bana na nufin kama baki na tsawon sa´o´i fiye da 16 a kowace rana. Shin yaya wuraren sayar da abinci da shagunan sayar da kayan abinci na musulmai suke tafiyar da aikinsu a cikin wannan wata a nan Jamus?

A yau za mu mayar da hankali ne akan azumin watan Ramadana a nan Jamus. A ƙarshen makon jiya ne al´umar musulmi a ko-ina cikin duniya suka fara wannan farali, ɗaya daga cikin shika-shikan addinin musulunci guda biyar. Ga musulmi masu bin dokokin addinin sau da ƙafa azumin na nufi kwanaki 30 babu cin abinci ko shan ruwa daga hudowar alfijir har zuwa faɗuwar rana. A wannan yankin na kusuwar arewacin duniya a bana musulmin na buƙatar juriya da ɗa´a ta musamman saboda yanayin da ake ciki na tsawon lokacin kama bakin wato kimanin sa´o´i 16 a rana. Masu sana´ar sayar da abinci na fuskantar wani ƙalubale cikin wannan wata.

Wannan wani gidan abinci ne na Turkawa dake wata unguwa da ta ƙunshi al´ummomi daban daban a birnin Kolon. Mai wurin Metin Dag ya ce yanayin watan azumin na da muhimmanci a gare shi maimakon watan kan sa. A saboda haka a bana ana kiran sallar Magaruba a gidan abincin nasa kafin a sha ruwa.

“A bana za mu yi ƙoƙarin kwaikwayon abin da ke faruwa a gida Turkiya wato ba za mu yi buɗe baki ba, har sai an yi kiran salla Magaruba, wato kenan don samun yanayi irin na Turkiya.”

Ba kamar mai gidanshi ba, shi kuwa matashi Murat Gök da ke aiki a gidan abincin ba ya wasa da sauke wannan farali. Lokacin da ya fara cika watan azumi kimanin shekaru bakwai da suka wuce, a lokacin sanyin hunturu ne, amma yanzu watan ramadana ya koma cikin lokacin zafi inda rana take da tsayi wato kimanin sa´o´i 16.

“A bana kan lokaci yayi tsayi, domin tun da misali ƙarfe huɗu da rabi na asuba muke kame baki har sai tara saura kwata kafin mu yi buɗe baki. Gaskiya da wuya. Ban sani ba ko zan iya cikawa. Mu dai sa ido mu ga ikon Allah.”

Azumin watan ramadana na zama ɗaya daga cikin shika-shikan addinin musulunci guda biyar kuma yana matsayin farali akan kowane musulmi, in ban da maras lafiya ko matafiyi.

To sai dai Murat Gök na ƙoƙarin yin azumin a cikin watan Ramadana domin kaucewa yin ramuwa bayan. Aikinsa dai na da wahalar gaske musamman a lokacin buɗe baki, domin sannan ne mutane ke zuwa gidan abincin don shan ruwa. Yayin da mutanen ke cin abinci shi kuwa dole ne ya ci-gaba da aikin sayar da abincin. Kasancewar yana sayar da abinci a duk tsawon rana Murat Gök bai damu ba. Ya ce abin damuwa shi ne idan ba aikin yi a gidan abincin.

“Ya fi kyau idan kana aiki, amma in zaman banza ka ke yi kuma ba zaka iya cin abinci ko shan ruwa ko shan taba ba, wallahi da wuya ƙwarai da gaske.”

Deutschland Restaurant Vapiano in Berlin
Hoto: picture alliance / dpa

Hatta a wannan shagon sayar da kayan abinci na ´yan ƙasar Marokko a birnin na Kolon ana ciniki sosai a cikin watan Ramadan. Younes Mahi shi ke kula da shagon da ya shahara wajen sayar da kayan abinci na ƙasashen Larabawa.

“A cikin watan Ramadana mutane sun fi cin abinci mai kyau, mai ba su lafiya. Saboda haka abincin da muke sayarwa a cikin watan azumi ya banbanta da na sauran watanni. Alal misali a cikin wannan wata na Ramadan muna sayar da abinci kala-kala waɗanda ba ma dafawa a sauran lokutan shekara.”

A cikin watan ana marmarin kayan lambu da alawa iri daban daban na ƙasashen Larabawa. To amma Younes Mahi ya ce jurewa yunwa ba wani abu ne mai wuyaa a gare shi domin shi ba mai son abinci ne sosai ba. Ya ce abin farin ciki a gare shi a wannan wata shi ne kasancewa ɗaya daga cikin babbar gamaiyar musulmi.

“Muna matuƙar maraba da wannan wata. A gare ni rana ta farko ce ke da wuya saboda sauyawan lokutan cin abinci na, na kan ji kasala. Amma bayan kwana biyu mko uku sai jiki na ya saba da wannan sauyin. Daga nan kuma sai gangara kawai.”

Murat Gök da Younes Mahi suna mayar da hankali sosai wajen sauke faralin na azumin Ramadan. To amma ba haka yake ga wasu musulmai mazauna wannan ƙasa ba. Wani bincike jin ra´ayin jama´a da babban taron musulmai a Jamus ya gudanar an gano cewa kimanin kashi 50 cikin 100 na ilahirin al´umar musulmai a Jamus suke azumin watan Ramadan. Nurhan Soykan ita ce sakatariyar yaɗa labaru ta Majalisar Tsakiyar Musulmin Jamus ta ce alƙalumman gaskiya ne.

“Ba na jin suna azumin har tsawon makonni huɗu, domin da yawa daga cikinsu wataƙila saboda dalilai na aiki ko makaranta, sun taƙaita sauke wannan farali zuwa ƙarshen mako kaɗai. Amma yawan waɗanda ba sa yin azumin gabaki ɗaya, ina jin ba zai haura kashi 30 cikin 100 ba.”

Iran Fastfood Restaurant in Teheran
Hoto: DW

Biyewa dokokin azumin ya danganta da gamaiyar musulmin da mutum yake a ciki. Alƙulumma sun nunar cewa yawan masu azumi a tsakanin ´yan Sunni a Jamus ya kai kashi 70 cikin 100 sannan a tsakanin ´yan ɗarikar Alawi yawansu ya kai kashi 20 cikin 100. Ko ka yi azumin ko kar ka yi, ga Murat Gök dai shan kunu buƙatar rai ne, kuma bai kamata ka yi katsalanda cikin abin da bai shafe ka.

“Yin wannan aikin farilla a nan Turai ya rage ne a gareka, domin babu mai ce ma ka yi ko kar ka yi. Ba wanda zai kwaɓe ka.”

Younes Mahi mai sayar da kayan abinci ya ce ba a amince da yin yin azumi ko ta halin ƙaƙa ba.

“Ba zaka iya tilastawa wani yin azumi ba. To amma yin azumin wata dama ce ta tsarkake zuciya da jiki. Idan zaka iya yi sai ka yi, idan ba zaka iya ba saboda wasu dalilai da shari´a ta yarda da su, sai ka ci abincin ka, ka yi ranko bayan watan Ramadan.

Kawo yanzu dai Younes Mahi na cika wata, kuma a kowace shekara yana fuskantar sabon ƙalubale.

Mawallafa: Martina Sabra/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi