Azabtar da Fursinoni a Iraki | Siyasa | DW | 06.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Azabtar da Fursinoni a Iraki

Hotuna da ake yayayatawa ta gidajen telebijin da jaridu sun zama kyakkyawar shaida a game da yadda sojojin Amurka suka rika gallazawa da kuma azabtar da fursinonin Iraki a gidajen kurkuku

Shaidar azabtar da fursinoni da sojan Amurka ke yi a Iraki

Shaidar azabtar da fursinoni da sojan Amurka ke yi a Iraki

A lokacin da aka tambayi albarkacin bakinsa a game da halin da ake ciki a Iraki wani da ake kira Karim Kazim cewa yayi:

An taba tsare ni a gidan kurkuku a zamanin mulkin Saddam hussein, kuma idan zan kwatanta da yadda lamarin yake a yanzu, sai in ce sojojin Amurka daidai suke da jami’an tsaron Saddam Hussein a matakai na rashin imani.

Wannan kuwa ra’ayi ne da akasarin manazarta al’amuran yau da kullum ke tattare da shi. Domin kuwa abin mamaki shi ne kasancewar tun a zamanin mulkin shugaba Saddam Hussein ne kurkukun Abu Ghoreib yayi kaurin suna wajen azabtar da fursinoni, kuma sai ga shi an wayi gari kurkukun ya sake zama dandalin tsangwama da azabtarwa na ba gaira ba dalili. Babu wani da zai musunta wannan batu saboda shaidar hotunan dake akwai. Wadannan hotuna sun tabbatar da gaskiyar korafin da kungiyoyin kare hakkin dan-Adam suka dade suna yi sakamakon cikakkun bayanan da suka samu daga tsaffin fursinoni. Shi ma Karim Kazem, karamin dan-tireda a birnin Bagadaza, an tsare shi tsawon watanni da dama a kurkukun na Abu Ghoreib, ya kuma yi wa tashar Deutsche Welle bayani dalla-dalla a game da azaba da cin mutunci da kuma keta huruminsa da sojojin Amurka suka yi tun bayan da sojojin Amurka suka tasa keyarsa zuwa kurkukun, inda ya kara da cewar:

Wasu sojoji ne guda hudu suka kwantar da ni, inda daya daga cikinsu ya take kaina, sannan suka rufe fuskata da wannan jakar suka kuma daure hannuwana. Har yau ina fama da tabon wannan cin mutunci da suka yi mini a zuciyata.

Ga alamu dai radadin wannan cin mutunci da keta huruminsa da aka yi ne ya sanya Karim Kazem yake i’ina lokacin da yake bayani, inda ya kara da cewar:

Da zarar sun rufe ma idanuwanka zaka rika ji tamkar ba ka da sauran mutunci kuma. Saboda ba wani mai sauraron kararka. A wani lokaci ni kan yi sa’o’i goma daure da wannan jaka a ka. Wasu daga cikin fursinonin ma sai su yi kwanaki uku a jere a cikin wannan mummunan hali na azaba. A tsakaninmu akwai wani dattiji mai sama da shekaru 50 da haifuwa dake fama da cutar hauhawar bugun jini. Wannan dattijo ya rasu sakamakon radadin azabar da kuma karayar zuciya. Shi kansa wannan mutumin sai da aka yi farautarsa a zamanin mulkin Saddam Hussein.

Wadannan bayanai na Karim Kazem da kuma hotunan da aka yada zuwa dukkan sassa na duniya a game da kurkukun Abu Ghoreib tamkar wata cikakkiyar shaida ce a game da halin da ake ciki a kasar Iraki yanzu haka. Abin tambaya a nan shi ne fursinoni nawa ne wannan mummunar ta’asa ta azabtarwa ta rutsa da su? Kuma ko shin magabatan sojojin Amurkan na da cikakkiyar masaniya game da haka? Ko kuma ma su ne suka ba da umarnin daukar wadannan matakai na keta haddin dan-Adam.