1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AZABTAD DA FURSUNONIN IRAQI RUWAN DARE NE GA DAKARUN AMIRKA, INJI RAHOTON HUKUMAR SOJIN KASAR.

YAHAYA AHMEDMay 4, 2004

Tun da aka ba da sanarwar azabtad da fursunonin Iraqi da dakarun Amirka ke yi ne, hukumar sojin kasar ta ce za ta dau matakan horo kan sojoji 7, da ake zarginsu da wannan aika-aika. Bugu da kari kuma ta ce ana binciken wasu `yan sandan soji guda 6, wadanda ake zaton suna da masaniya game da rashin imanin da sojojin ke aikatawa kan fursunonin Iraqin. Amma har ila yau, babu tabbacin cewa, za a gabatad da su gaban kotun sojin don yi musu shari’a.

https://p.dw.com/p/Bvk1
Sojojin Amirka, gaban fursunonin Iraqi da suka tube tsirara, suna nuna musu cin mutunci da wulakanci.
Sojojin Amirka, gaban fursunonin Iraqi da suka tube tsirara, suna nuna musu cin mutunci da wulakanci.Hoto: AP/Courtesy of The New Yorker

Wani rahoto, kan binciken da Hukumar sojin Amirka ta gudanar, wanda kuma jaridar nan ta New York Times ta buga jiya, game da azabtad da fursunonin Iraqi, da dakarun Amirkan ke tsare da su a gidan yarin Abu Gharib a birnin Bagadaza, na nuna cewa, ba wasu tsirarun sojoji kawai ne ke wannan danyen aikin ba, kamar yadda mahukuntan Amirkan ke kokarin bayyana wa duniya. Wannan halin ya zame wa duk masu gadin wannan gidan yarin jiki. Kowa kuma na iya nuna wa fursunonin irin azabar da ya ga dama, inji rahoton.

Amma duk da hakan, kakakin rundunar sojin Amirka a Iraqin, Birgediya-Janar Mark Kimmit, ya ci gaba da nanata cewa, wasu `yan tsirarun sojoji ne kawai suka yi abin da yake kira "wannan kuskuren":-

"Bayan dai duk abin da muka sani game da binciken da aka gudanar kawo yanzu, mutane 6 ne kawai za a yi musu shari’a, sa’annan a dau matakan horo kan wasu 10 kuma. A nawa ganin dai, wannan lamarin, takaitacce ne, idan aka yi la’akari da dubannin fursunonin da suke daure a gidan yarin Abu Gharib da kuma darurukan jami’an da alhakin kula da su ya rataya a wuyarsu."

Ba dai sojojin Amirkan ne kawai ke aikata wannan ta’asar ba. Jami’an kungiyoyin leken asirin Amirkan da kuma kamfanoni masu zaman kansu, wadanda aka bai wa kwangilar gudanad da bincike kan fursunonin, su ma suna da hannu dumu-dumu wajen gudanad da wannan danyen aikin. Wani daya daga cikin sojojin Amirkan da ake zarginsu da nuna wa fursunonin azaba, Sajin Chip Frederick, ya mika wa baffansa, William Lawson, rubuce-rubucen da ya yi kan irin cin mutuncin da suke yi wa fursunonin. Lawson din ya bayyana wa maneman labarai cewa:-

"Sojojin da aka dora wa nauyin kula da fursunonin, na duk iyakacin kokarinsu, wajen samun umarni daga shugabanninsu kan yadda za su yi musu bincike. Amma ba sa samun ko wane umarni daga sama. Sai dai ce musu ake yi, su aiwatad da duk umarnin da kamfanonin tsaro masu zaman kansu, za su ba su. Umarnin wadannan kamfanonin kuwa, sun hada ne da nuna wa fursunonin mummunar azaba kafin a shiga yi musu tambayoyi."

Ma’aiktar tsaron Amirkan dai, wato Pentagon, ta bai wa dimbin yawan kamfanonin tsaro masu zaman kansu kwangila a Iraqin. Su wadannan kamfanonin kuwa, ba sa karkashin wata hukumar soji. Shi ya sa abin da suka ga dama suke yi. Manyan jami’an siyasar Amirkan da dama ne suka nuna bacin ransu matuka gáayàa, game da rahotannin azabtad da fursunonin Iraqin da dakarunsu ke yi. `Yan siyasa, kamar dai senatan jam’iyyar Demokrat din nan mai angizo, John Biden, ya bayyana fargabar da yake yi, ta cewar, wannan danyen aikin dai zai janyo wa Amirka wani gagarrumin cikas, ya kuma shafa wa sunanta kashin kaza a duniya baki daya. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

"Tun fiye da shekaru 10 da suka wuce, babu wani abin da ya taba janyo dusashewar kwarjininmu da kuma gagarumin cikas ga maslaharmu a wannan yanki na duniya, kamar wannan batun."