1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan tarzoma tsakanin Amurkawa

January 7, 2010

Manazartan Amurka sun fara nuna damuwa dangane da karuwan 'yan ta'adda Amurkawa matasa

https://p.dw.com/p/LNfG
Ta'addanciHoto: AP

Mutumin da ake zargi da shirya hare-haren birnin Mumbai na Indiya, da kuma wanda ya kai hari a sansanin sojin Amurka na Fort Hood, na zama ƙalilan daga cikin Amurkawa masu tsananin kishin addinin Islama, dake da alaka da ƙungiyar Alqaida. Adangane da hakane ƙwararru ke cigaba da gargaɗi dangane da irin barazanar da Amurka ke fuskanta daga cikin al'ummarta.

"Ya zamanto wajibi mu mayar da hankali kan sabbin barazana. Bayan wata barazanar harin ta'addanci daga cikin ƙasarmu, da kuma sabbin 'yan ta'adda na zamani da ke ɗauke da takardar Passport ɗin Amuraka.."

US-Heimatschutzminister Michael Chertoff vor Abflug nach Louisiana
Michael ChertoffHoto: AP

Tsohon shugaban sashin kula da harkokin tsaron cikin gidan Amurka Michael Chertoff ke nan ke gargaɗi.

'Yan asalin Amurka da aiwatar da hare-hare akan Amurka da ma Duniya baki ɗaya, wannan shine babban abun tsoro da gwamnatin Obama ke fuskanta.

"Wannan kira ne na bukatar tashi tsaye..."

Wannan dai wani kira ne na faɗakarwa a daga gidan talabijin ɗin CBS. Fiye da shekara guda bayan da masu tsananin ƙishin addinin Islama kuma Amurkawa suka ingiza harin daya zubar da jini, a ciki da wajen Amurkan. Alal misali, David Coleman Headley, Baamurke dake da asalin Pakistan, wanda kuma yake cikin waɗanda hukumar leken asirin Amurka ta ke binci dangane da shirya harin da aka kai a cibiyar cinikin Indiya ta Mumbai, wanda ya kashe mutane 107, ciki harda Amurkawa guda 6.

Kafofin yaɗa labarun Amurka dai sun ruwaito cewar, David Coleman Headley, ya taimaka wajen tsara harin na Munbai ne daga birnin Chicago. Ya ɗauki tsawon shekaru dai yana hulɗa ta yanar gizo da 'yan gani kashenin Al-Qaida a Pakistan. Tare da ziyartar Mumbai domin nazarin otel-otel guda biyar, domin kai hari.

An dai gabatar da hotonan David Headley a lokacin daya je Mumbai, da yada zangon da yayi a kasar Pakistan, da kuma irin mutanen daya tuntuɓa, dangane da shirin kai harin, kafin ya koma birnin Chicago.

Wani misali shine Nadal Malik Hassan , wani jami'in soji musulmi Baamurke, wanda ya kai hari a sansanin sojin Fort Hood daya kashe mutane 13, har da shi kansa , baya ga wasu 30 da suka jikkata.

Da yawa daga cikin kalaman Hassan dai sun danganta ƙiyayyar da Amurkan ke fuskanta tsakanin Amurkawa kansu da yaƙe-yaƙen data kaddamar akan Afganistan da Iraki, dake zama ƙasashen musulmi.

Sakamakon yaƙin da aka kaddamar akan ƙasarsu ta asali ne ya sanya, wasu matasa Amurkawa guda biyar daga jihar Virginia, suka kaura zuwa Pakistan, wanda gabannin nan sai da suka gabatar da hoton video na bankwana.

Terror Detroit Flughafen
Hoto: AP

" Wannan Video yayi matukar tayar min da hankali"

Waɗannan su ne kalaman Imam Abkir, ɗaya daga cikin manyan malaman al'ummar musulmin Virginia.

Ya bayyana damuwansa dangane da yadda Kungiyar Al-Qaida ke cigaba da yin tasiri ta yanar gizo tsakanin Amurkawa musulmi masu yawa. Adangane da haka ne Imam Abkir yayi kira ga hukumomin tsaron Amurka dasu mayar da hankali sosai kan shafin yanar gizon masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama, musamman wanda yara matasa ke yawaita karantawa.

Daura da hakan Limamin yayi kira ga dukkan al'ummomin musulmi da su rika la'akari da dukkan abubuwan da ke gudana a masallatansu.

Mawallafa:Zainab Mohammed/Sina Ralf

Edita: Umaru Aliyu