Ayyukan da hukumar zuba jari da raya kasa ta Jamus ta yi a shekara ta 2003. | Siyasa | DW | 21.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ayyukan da hukumar zuba jari da raya kasa ta Jamus ta yi a shekara ta 2003.

Duk da matsalolin tattalin arzikin duniya sakamakon yakin kasar Iraqi da annobar cutar SARS a nahiyar Asiya da rikicin siyasa da na tattalin arziki a yankin Latunamirka, hukumar zuba jari da raya kasa ta tarayyar Jamus wato DEG ta bayyana shekarar da ta wuce a matsayin shekarar da ta samu nasarar gudanar da ayyukanta. Kudi kimanin Euro miliyan 506 da hukumar ta bayar don zuba jari da raya kasa a kasashe masu tasowa ya kasance mafi yawa da hukumar ta DEG ta taba kashewa a cikin tarihin ta na shekaru 41 da kafuwa. Yanzu haka dai wannan hukuma ita ce mafi girma a jerin hukumomi da kungiyoyin ba da taimakon raya kasa da zuba jari a Turai. Babbar manufar wannna hukuma dai shine yaki da talauci.

Kakakin hukumar ta DEG Winfried Polt ya ce muhimman abubuwan da hukumar sa ke yi sun hada da samar da sabbin guraben aikin yi don samar da kudaden shiga ga jama´a, da taimakawa kasa ta samu rancen kudi. Hukumar na taimakawa a fannonin kiwon lafiya, sufuri da ba da ilimi.

Baya ga taimakon da ta ke ba matsakaitan kamfanonin Jamus dake zuba jari a ketare, hukumar ta DEG na taimakawa kamfanoni a kasashen da ke kawance da ita. Wannan gudummawa da hukumar ke ba kamfanoni masu zaman kansu na taka muhimmiyar rawa wajen inganta halin rayuwar jama´a. Alal misali hukumar ta cimma yarjejeniya da kamfanonin da take taimaka musu da su tanadarwa ma´aikatansu tsarin kiwon lafiya kyauta tare da samar musu magunguna da rahusa.

A fannin muhali ma hukumar ta DEG na mayar da hankali sosai, inda ta ke shimfida sharudda masu tsauri game da kare muhalli kafin ta ba da taimako.

A halin da ake ciki nahiyar Asiya ce ke kan gaba a jerin yankunan da hukumar ta DEG ta fi gudanar da ayyukanta, inda a kasar Sin kadai, wadda a halin yanzu take samun bunkasar tattalin arziki, hukumar ta gudanar da ayyukan da kudinsu ya kai Euro miliyan 18.

Yankin da ke matsayi na biyu shine na gabashin nahiyar Turai, musamman a kasashen da ke jeri na biyu cikin kasashen da za´a shigar da su cikin kungiyar tarayyar Turai EU, wato kamar Romaniya da Kuratiya. A bara nahiyar Asiya da yankin gabashin Turai sun kasance wurare da suka fi jan hankalin kamfanonin Jamus musamman dangane da bunkasar tattalin arzikin da ake samu a wadannan wurare.

Nahiyar Afirka da yankin Latunamirka har wayau ana musu kallon wuraren da babu tabbas a ciki. To amma duk da haka a bara hukumar ta DEG ta gudanar da ayyuka masu tarin yawa a wadannan yankuna. A kuma halin da ake ciki rangadin da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ke kaiwa nahiyar Afirka, zai taimaka wajen daga darajar wannan nahiya a manufar gwamnatin Jamus. A cikin shekarar da ta gabata hukumar DEG ta zuba jari da ya kai Euro miliyan 80 a wannan nahiya, musamman a kasashen ATK, Mozambique, Kenya da kuma Nijeriya. Haka zalika wani binciken samar da maganin gargajiya da hukumar ke yi a kasar Masar ya samu kyautar yabo ta Nobel.
 • Kwanan wata 21.01.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmP
 • Kwanan wata 21.01.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmP