Ayarin Dakarun Burundi na biyu sun isa Somalia | Labarai | DW | 24.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ayarin Dakarun Burundi na biyu sun isa Somalia

Ayari na biyu na dakarun kasar Burundi sun isa ƙasar somalia.Ayarin daya ƙunshi jami’an sojin Burundin kimanin 92 dai ,na ɓangaren ayarin dakarun ƙasashen Afrika da zasu je ƙasar domin taikamaka samar da zaman lafiya,a wannan ƙasa dake yankin kahon Afrika.Ɗauke da bindigogi kirar Ak-47 dai,dakarun sun isa sansanin dakarun kungiyar ta AU ne ,bayan sauka daga jirgin saman Uganda,wanda ke kusa filin saukan jiragen sama na birnin Mogadishu.Commandan rundunar Afrika Major General Levi Karuhanga,ya bayyana farin cikin sa dangane da isan ayarin na Burundi Somalia.Daga nan ne yayi kira ga sauran ƙasashen Afrika dasu cikanta alkawura da suka ɗauka na aikewa da dakarunsu,ta hanyar yin koyi da Burundi data tura ayari biyu .