Austreliya ta tura dakaru zuwa yankin gabashin Timor. | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Austreliya ta tura dakaru zuwa yankin gabashin Timor.

Austreliya ta gaggauta tura dakaru dubu da ɗari 3 zuwa gabashin Timor, sakamakon taɓarbarewar halin da ake ciki a ƙasar, bayan wani boren da wasu dakarun rundunar sojin ƙasar suka tayar. Yau da safen nan ne dai farkon rukunin dakarun Austreliyan, da ya ƙunshi sojojin ƙundumbala 150, ya isa a birnin Dili, wato babban birnin ƙasar. Tuni dai, wani jirgin ruwan yaƙin Austreliyan, ya jefa anka a tashar jirgin ruwan birnin na Dili, inda yake jiran umarnin bai wa sojojin da ke ciki damar sauka a ƙasa.

A halin da ake ciki kuma, rahotanni sun ce ƙarin dakaru daga Portugal, da Malesiya da New Zealand na kan hanyarsu zuwa ƙasar ta Gabashin Timor. Hakan dai ya biyo bayan kiran taimako ga gamayyar ƙasa da ƙasa ne da gwamnatin ƙasar ta yi.

Kawo yanzu dai, a ƙalla mutane 6 ne suka rasa rayukansu, tun da rikicin ya ɓarke a farkon wannan makon a ƙasar.